Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun yi garkuwa d 'yan mata 2

Katsina: 'Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun yi garkuwa d 'yan mata 2

An gano cewa mutum 3 sun rasa rayukansu a kauyen Maitsani da ke karamar hukumar Dutsin-Ma ta Katsina tare da sace 'yan mata biyu a garin Kurfi da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda jama'ar yankin suka sanar, wadanda aka kashe sune: Sada Sani da Shuaibu Abubakar, yayin da Sani Turare ya rasu sakamakon raunikan da ya samu a babban asibitin Dutsin-Ma.

'Yan bindiga sun kai hari kauyen a ranar Asabar inda suka dinga harbe-harbe tare da raunata jama'a.

Sun kwashe tumaki da shanu yayin da za su wuce.

Hakazalika, a daren Lahadi, wasu wadanda ake zargin 'yan bindiga ne sun tsinkayi Sabuwar Unguwa da ke Sabon Layi a karamar hukumar Kurfi inda suka sace 'yan mata biyu. Sun dauke Nana Firdausi Sani mai shekaru 17 da Fauziya Sani mai shekaru 24.

Jama'ar yankin sun ce, masu garkuwa da mutanen sun isa garin da karfe 2 na dare tare da sace 'yan matan bayan sun samu shiga gidansu.

Har a yanzu 'yan sands basu yi martani a kan al'amarin ba.

KU KARANTA: Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana

A wani labari na daban, a kalla mutum 20 suka rasu sakamakon harin 'yan bindiga a garin Chibuak da Kigudu da ke karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

An kai hari kauyukan biyu ne a ranakun Alhamis da Jama'a da suka gabata amma a tsakar dare. Wasu daga cikin mazauna kauyen sun bace.

'Yan bindigan sun sake kai hari a ranar Asabar a Kigudu yayin da mazauna kauyen ke shirin birne matan mabiya addinin kirista kuma akidar Katolika.

Amma kuma jami'an tsaro sun fatattaki 'yan bindigar sannan aka gaggauta birne mamatan. Babban fasto, Rabaren Aaron Tanko, wanda shi ke jagorantar yankunan biyu, ya tabbatar wa da manema labarai cewa mutum 20 ne suka rasu yayin da wasu suka bace.

Ya ce a kauyen Chibuak, mutum 9 ne suka rasu yayin da aka kashe 11 a kauyen Kigudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel