Buhari ya taya Usman murnar zama shagon gasar damben UFC

Buhari ya taya Usman murnar zama shagon gasar damben UFC

- Shugaban kasa Muhammadu ya taya Kamarudeen Usman murnar sake lashe gasar damben 'Ultimate Fighting Championship' UFC

- Buhari ya ce Usman ya tunatar da duniya cewa har yanzu Nigeria na kyankyasar abubuwa masu kyau da kuma nagartattun mutane

- Usman ya samu nasarar kare wannan kambun nasa ne bayan da ya kara da Jorge Masvidal, ya kuma samu nasara a kansa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, ya taya Kamarudeen Usman murnar sake lashe gasar damben 'Ultimate Fighting Championship' UFC, yana mai cewa wannan nasarar ta kara daga martabar 'yan Nigeria tare da kara masu kaimi duk da irin matsalolin da annobar Covid 19 ta haddasawa kasar.

Tayar murnar da shugaban kasa Buhari ya yi, na dauke ne a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara kan kafofin sada zumunta na zamani da kuma wasa labarai, Femi Adesina wacce kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar na dauke da taken: "Shugaban kasa Buhari ya taya Kamaru Usman murnar kare kambunsa na shagon gasar damben UFC"

Usman ya samu nasarar kare wannan kambun nasa ne bayan da ya kara da Jorge Masvidal, ya kuma samu nasara a kansa.

KARANTA WANNAN: 'Na yi lalata da yaro ne saboda sha'awa ta takurani bayan na sha jike - jike' - Bello

Buhari ya taya Usman murnar zama shagon gasar damben UFC
Source: Twitter
Buhari ya taya Usman murnar zama shagon gasar damben UFC Source: Twitter
Asali: Instagram

Da wannan nasarar, Buhari ya ce Usman ya tunatar da duniya cewa har yanzu Nigeria na kyankyasar abubuwa masu kyau da kuma nagartattun mutane da ke taka rawa ta kowanne fanni na rayuwa.

Ya kara da cewa nasarar da Usman ya samu ta kara jaddadawa duniya cewar komai zai dawo dai dai, musamman a wannan gabar da kasar ke son ganin ta cimma muradunta.

Sanarwar na cewa: "A matsayinsa na d'an Afrika na farko kuma d'an Nigeria mai rike da kambun gasar damben UFC, shugaban kasa Buhari na jinjinawa wannan jarumi a nasarar da ya samu, da kuma fitar da 'yan Nigeria a idon duniya, da kuma tunasar da duniya cewa har yanzu Nigeria na kyankyashe abubuwa masu kyau da kuma nagartattun mutane.

"A yayin da annobar Covid-19 ta kawo nakasu ga iyalai da ma kasa baki daya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jin dadinsa kan wannan nasarar domin a cewarsa ta daga daraja da tasirin zukatan 'yan Nigeria, da kuma yin nuni da cewar nasarar alama ce ta cewar abubuwa zasu dawo dai dai musamman a wannan lokacin da kasar ke son cimma muradun da ta sanya a gabanta.

"Shugaban kasar ya kuma yiwa Usman fatan alkairi da kuma fatan samun nasarori a wasanninsa na gaba."

A wani labarin, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Jami'an hukumar NSCDC sun kama wani matashi Yusuf Bello, mai shekaru 25, bisa zarginsa da aikata lalata da wani karamin yaro mai shekaru 11.

Jami'an tsaron sun kama matashin ne a garin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

Da ya ke jawabi ga manema labarai yayin bajakolin ma su laifi a hedikwatar rundunar, kwamandan NSCDC a jihar Nasarawa, Dakta Muhammad Mahmoud Fari, ya ce an kama Bello jim kadan bayan aikata laifin.

Da ya ke amsa laifinsa, Bello ya zargi wani maganin gargajiya da ya sha da tunzura shi wajen haikewa karamin yaron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel