Cikin kwanaki 3 an kashe mutane 22 a Kudancin Kaduna - SOKAPU

Cikin kwanaki 3 an kashe mutane 22 a Kudancin Kaduna - SOKAPU

Kungiyar Al'ummar Kudancin Kaduna SOKAPU, a ranar Lahadin da ta gabata ta yi ikirarin cewa, akalla rayukan mutane 22 sun salwanta a hare-haren da 'yan bindiga suka rika kai musu tsawon kwanaki uku.

A cewar kungiyar, kananan hukumomin da hare-haren suka shafa sun hadar da Kauru, Zangon-Kataf da kuma Kajuru.

SOKAPU ta ce wannan lamari ya auku duk da dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta shimfida a biyu daga cikin kananan hukumomin.

Babban jami'in hulda da al'umma na kungiyar, Luka Binniyat, shi ne ya zayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Ya ce ana zargin Fulani makiyaya ke da hannu a hare-haren.

Kungiyar ta SOKAPU ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da wani tallafi ga wadanda rikicin ya ritsa da su domin rage musu radadi da kuma halin kunci da suka tsinci kansu.

Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna; Mallam Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa, "harin farko ya auku ne da misalin karfe 1.30 na daren ranar Juma'a, inda makiyaya suka mamaye kauyen Chibob na garin Gora da ke karkashin karamar hukumar Zangon Kataf."

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a yayin aukuwar wannan hari, rayukan mutane 9 sun salwanta wanda kuma galibinsu mata ne da kananan yara.

"Baya ga yin awon gaba da kayan abinci, maharan sun kuma ƙone fiye da gidaje 20 tare da lalata gonaki da dama yayin da kuma suka yi awon gaba da shanu 24 da sauran dabbobin kiwo."

KARANTA KUMA: WAEC: Iyayen dalibai za su gana da gwamnatin tarayya a ranar Litinin

"A yayin da dokar hana zirga-zirga ta tsananta a ranar Asabar, makiyayan na Fulani sun sake kai wani mummunan hari kan al'ummar Kigudu da ke maƙwabtaka da garin Chibob wanda ya yi iyaka da kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru."

"Wannan hari ya salwantar da rayukan mata 10, jariri daya da wani dattijo guda daya yayin da aka ƙone su ƙurmus a wani gida da suka labe wajen neman mafaka a cikinsa."

"Wasu daga cikin gawawwakin da aka ƙone sun zama toka. An ƙone gidaje hudu. Wanda wannan ya kawo adadin mutane 12 kenan da suka halaka."

Haka kuma da sanyin safiyar ranar Lahadi, maharan sun kutsa kauyen Surubu da ke garin Gora, inda bayan sun yashewa al'umma dukiya, sun kuma ƙone musu gidaje tare da kashe mutum daya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel