Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana

Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana

Hedkwatar tsaro ta ce sojin sama na rundunar Operation Hadarin Daji, sun karar da wasu 'yan bindiga a harin da suka kai sansaninsu a wani bangare na dajin Kuyambana da ke jihar Zamfara a ranar 10 ga watan Yulin 2020.

Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana
Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

Shugaban bangaren yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Enenche ya ce harin ya biyo bayan gano wasu gidajen da aka gina a cikin surkukin dajin wanda ake tsammanin mayakan ISWAP da 'yan bindiga karkashin kungiyar Dogo Gede ke amfani da su.

Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana
Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

Kamar yadda yace, an tura jiragen yakin sojin saman da jirgin sama mai dauke da bindigogi don tarwatsa wurin.

Takardar ta ce, "Jiragen yakin sun dinga sakin musu ruwan wuta har sai da sansanin 'yan ta'addan ya tarwatse sannan wasu 'yan bindigar suka halaka.

Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana
Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

"Wasu 'yan bindigar da aka gani suna kokarin tserewa a kan babura 15 an kashesu da jiragen yaki.

"Daga bisani an gano cewa 'yan bindigar masu tarin yawa sun halaka kuma baburansu sun kone sakamakon harin jiragen yakin."

Takardar ta ce, shugaban dakarun sojin saman, Air Marshal Sadique Abubakar ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Daji a kan kwarewarsu.

Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana
Hotuna da Bidiyo: Sojin sama sun ragargaza maboyar 'yan bindiga da ISWAP a dajin Kuyambana. Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

Ya horesu da su ci gaba da ayyukan su na tarwatsa 'yan ta'addan ta sama wanda hakan ke samar da babbar nasara wurin karar da 'yan bindigar.

KU KARANTA: Zargin rufa-rufa: 'Yan daba sun kutsa ofishin NFIU, sun ragargaza kwamfutoci

A wani rahoto na daban, R=rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutum 3 da aka yi garkuwa dasu a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce dakarun sojin ne karkashin rundunar Operation Thunder Strike na kasan Operation Accord, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kakakin rundunar ya yi bayanin cewa bayanan sirrin da sojojin suka samu ne na cewa 'yan bindiga sun sace wasu mutane a gonarsu da ke kauyen Gwazunu, yasa suka bi sahu.

Ya kara da cewa jami'an tsaro da aka tura da gaggawa ne suka yi musayar wuta tsakaninsu da 'yan bindigar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel