Jagoran mafarautan Borno ya fada tarkon garkuwa ta 'yan Boko Haram

Jagoran mafarautan Borno ya fada tarkon garkuwa ta 'yan Boko Haram

Mun samu rahoton cewa, shugaban mafarauta a jihar Borno, Abdulkareem Umar wanda aka fi sani da Baba Mai Giwa, ya fada tarkon garkuwa ta mayakan Boko Haram.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Baba Mai Giwa ya kasance na hannu daman rundunar dakarun sojin Najeriya da ke matukar taya ta yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa, ana zargin reshen kungiyar mayakan Boko Haram wanda Modu Sulum ke jagoranci, su ne suka yi garkuwa da Baba Mai Giwa saboda rashin cimma matsayar wata yarjejeniya.

Baba Mai Giwa na daya daga cikin daruruwan mafarauta da gwamnatin Borno a shekarar da ta gabata ta rataya wa nauyin agazawa dakarun sojin a fagen yaki da masu tayar da kayar baya na Boko Haram.

Mayakan Boko Haram
Hoto Daga Jaridar Daily Trust
Mayakan Boko Haram Hoto Daga Jaridar Daily Trust
Asali: Twitter

Babu shakka Baba Mai Giwa ya shahara musamman bayan da ya jagoranci mafarautan da suka taimakawa gwamnatin jihar Bauchi a lokacin mulkin Gwamna Isa Yuguda, ta dakile ta'addancin mayakan Boko Haram a shekarar 2009.

Haka zalika a jihar Borno, Baba Mai Giwa shi ne ke jan ragamar fiye da mafarauta da 'yan sa-kai 5000 masu taya rundunar soji kai hare-hare a kan mayakan Boko Haram.

Wata majiya ta bayyana cewa, Baba Mai Giwa ya fara kulla yarjejeniya da wani reshe daya na mayakan Boko Haram, inda aka sanya lokacin haduwa a yayin da tattaunawarsu ta girmama.

KARANTA KUMA: Mu tsamo nahiyar mu daga kangin rashawa - Buhari ya gargadi shugabannin Afrika

Majiyar ta bayyana cewa: "Modu Sulum ya yi alkawar ajiya makamansu tare da daruruwa mayakansu domin rungumar zaman lafiya."

"Wasu daga cikin bukatun da jagoran mayakan ya gabatar su ne gwamnati ta yi musu afuwa kuma ta ba su damar dawo da zama tare da al'umma cikin lumana da aminci."

"Sun kuma bukaci a yi musu tanadin muhallai da sauran abubuwan da za su dogara da su na rayuwar yau da kullum."

"Duk wannan Baba Mai Giwa ne ya sha alwashin zai shiga tsakani wajen kulla yarjejeniya da neman sasanci."

"Modu Sulum ya kuma nemi masu sasancin su kawo musu tif din tayun keke guda 15 da sauran ababen yayin zuwansu kulla yarjejeniya a sansanin masu tayar da kayar bayan da ke mahadar Borzoggo."

"A yayin da suka fita neman sasanci tun a ranar 4 ga watan Yuli, mayakan su sauya niyyarsu, kuma suka yi garkuwa da Baba Mai Giwa da wasu mafarauta biyu da suka yi rakiyarsa."

"Tun daga wannan lokaci har kawo yanzu, ba mu sake jin duriyar Baba Mai Giwa ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: