Ba za mu bude makarantu ba har sai mun tabbatar da amincin aiwatar da hakan - Jihohin Arewa

Ba za mu bude makarantu ba har sai mun tabbatar da amincin aiwatar da hakan - Jihohin Arewa

A yayin da likafar annobar korona ke ci gaba, kwamishinonin Ilimi na jihohin Arewa 19 sun yanke shawarar buɗe makarantu da zarar sun tabbatar da amincin aiwatar da hakan.

Bayan ganarwa da suka yi ta yanar gizo, kwamishinonin ilimin cikin wata sanar da suka gabatar cikin garin Kaduna a ranar Asabar, sun yi la'akari da yiwuwar buɗe makarantu da sauran ababe na inganta sashen ilimi.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Dakta Shehu Makarfi, shi ne ya rattaba hannu kan wannan sanar da kwamishinonin suka fitar.

Dalibai
Hoto daga Premium Times
Dalibai Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

Wannan taro ya samu halarcin kwamishinoni 13 daga cikin jihohin Arewa 19 da suka hadar da; Kaduna, Bauchi, Gombe, Neja, Nasarawa, Adamawa, Taraba, Kogi, Kwara, Katsina, Kano, Borno da kuma Jigawa.

A yayin da suke mara masa baya, kwamishinonin sun yaba wa Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, dangane da hukuncin da ya yanke na haramta buɗe makarantu a yanzu.

A cewarsu, ci gaba da kasancewar makarantu a rufe a halin yanzu duba da yadda cutar korona ke ci gaba da yaduwa a fadin kasar, ita ce babbar mafita ta tabbatar da zaman dalibai cikin aminci.

Legit.ng ta ruwaito cewa, cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana, ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 664 da cutar korona ta harba a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Binciken Magu da sauran manyan abubuwa 2 da suka wakana a makon jiya

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter a daren ranar Asabar, 11 ga watan Yuli, 2020.

NCDC ta fitar da jerin jihohi da jimillar karin mutanen da suka harbu a jihohin kamar haka; Lagos-224, Abuja-105, Edo-85, Ondo-64, Kaduna-32, Imo-27, Osun-19, Filato-17, Oyo-17, Ogun-17, Rivers-14, Delta-11, Adamawa-10, Enugu-7, Nassarawa-6, Gombe-3, Abia-3, Ekiti-3.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:46 na daren ranar Asabar akwai jimillar mutane 31987 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel