Abubuwa 5 da fadar shugaban kasa ta furta game da binciken Magu

Abubuwa 5 da fadar shugaban kasa ta furta game da binciken Magu

Kimanin kwananaki da fara bincike a kan Ibrahim Magu, fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa game da bincken.

'Yan Najeriya da dama sun yi tir a kan rashin cewa komai da fadar shugaban kasar ta yi na tsawon lokaci musamman yadda mabanbantan rahotanni suka cika kafafen watsa labarai.

Tun bayan da aka tsare Magu domin ya amsa tambayoyi, sanarwar da ta fito a hukumance ita ce wadda ministan sharia kuma atoni janar na kasa, Abubakar Malami, SAN, ya fitar.

Abubuwa 5 da fadar shugaban kasa ta ce game da binciken Magu
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Sanarwar ta Malami ta tabbatar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Magu da kuma maye gurbinsa da Mohammed Umar, Shugaban sashin ayyuka na EFCC.

Fadar shugaban kasar kuma ta fitar da sanarwa a kan binciken da ake gudanarwa a kan dakatataccen shugaban na EFCC, a ranar Asabar 11 ga watan Yuli.

DUBA WANNAN: Hotunan hatsabiban ƴan bindiga da sojoji suka kashe a Arufu

Legit.ng ta tsamo wasu daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin sanarwar da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar.

1. Binciken ba Magu kadai ta shafa ba, ta shafi wasu maaikatan hukumar EFCC

Duk da cewa sunan mukadashin shugaban EFCC, Magu ne aka fi ji a binciken, ba shi kadai ne ake zargi da aikata ba daidai ba. Sanarwar ta ce an kaddamar da binciken ne sakamakon zargi da aka yi a kan Magu da wasu maaikatan hukumar.

2. Dakatar da Magu

Fadar shugaban kasa ta ce dakatar da Magu wani mataki ne da aka dauka domin a tabbatar da an gudanar da sahihin bincike ta yadda ba zai iya amfani da kujerarsa ba don yin katsalandan ga binciken.

3. Kwamitin binciken shugaban kasar hallastaciya ce

Yayin da wasu ke ganin kamar kotu ya dace kawai a gurfanar da Magu a maimakon kafa kwamitin bincike, fadar shugaban kasar ta ce akwai hurumin kafa kwamitin a dokar kasa saboda haka ba saba doka bane.

4. An bawa Magu damar ya kare kansa

Sanarwar ta fadar shugaban kasa kuma ta ce an bawa dakataccen shugaban na EFCC ikon ya kare kansa daga zargin da ake masa.

5. Binciken Magu alama ce da ke nuna yaki da rashawa da gaske ne

Akasin wasu rahotanni da ke cewa binciken Magu alama ce da ke nuna yaki da rashawa ta gwamnatin Buhari tana rushe wa, fadar shugaban kasar ta ce binciken ya nuna cewa yaki da rashawar gaskiya ne kuma babu wanda ya fi karfin doka.

Sanarwar ta jadada cewa binciken Magu ya nuna cewa, "babu shafaffu da mai" a yaki da rashawar da gwamnatin Buhari ke yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel