Kaduna: A kalla mutum 20 sun rasa ransu a harin 'yan bindiga

Kaduna: A kalla mutum 20 sun rasa ransu a harin 'yan bindiga

A kalla mutum 20 suka rasu sakamakon harin 'yan bindiga a garin Chibuak da Kigudu da ke karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

An kai hari kauyukan biyu ne a ranakun Alhamis da Jama'a da suka gabata amma a tsakar dare. Wasu daga cikin mazauna kauyen sun bace.

'Yan bindigan sun sake kai hari a ranar Asabar a Kigudu yayin da mazauna kauyen ke shirin birne matan mabiya addinin kirista kuma akidar Katolika.

Amma kuma jami'an tsaro sun fatattaki 'yan bindigar sannan aka gaggauta birne mamatan.

Babban fasto, Rabaren Aaron Tanko, wanda shi ke jagorantar yankunan biyu, ya tabbatar wa da manema labarai cewa mutum 20 ne suka rasu yayin da wasu suka bace.

Ya ce a kauyen Chibuak, mutum 9 ne suka rasu yayin da aka kashe 11 a kauyen Kigudu.

Kamar yadda yace, "An kawo harin a tsakar daren Alhamis da Juma'a.

"An kai harin Chibuak a ranar Alhamis inda suka kashe mutum 9. An kai harin Kigudu a ranar Juma'a inda aka kashe mutum11.

"Wasu mazauna kauyen sun bace don haka babu tabbacin yawan mutanen da suka rasu.

Kaduna: A kalla mutum 20 sun rasa ransu a harin 'yan bindiga
Kaduna: A kalla mutum 20 sun rasa ransu a harin 'yan bindiga. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zargin rufa-rufa: 'Yan daba sun kutsa ofishin NFIU, sun ragargaza kwamfutoci

"Muna tsaka da shirin birne su a ranar Asabar a Kigudu, amma sai ga makiyaya sun kawo mana hari. Sai dai jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakar su.

"Ba a sake kashe kowa ba ko kuma raunatawa.

"Ko yadda ya dace bamu bi ba wurin birnesu. Mun yi gaggawa domin gujewa dawowarsu.

"Suna zuwa da makamai kuma su yi ta kashe jama'a yadda suka so. Yanzu haka akwai kauyukan da jama'a basu iya zuwa noma saboda tsoron makiyaya.

"Muna kira ga gwamnati da ta dauka mataki a kan wannan hali da muke ciki."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammad Jalige, ya ce zai samo bayanin al'amarin kafin ya yi tsokaci.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto mutum 3 da aka yi garkuwa dasu a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce dakarun sojin ne karkashin rundunar Operation Thunder Strike na kasan Operation Accord, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kakakin rundunar ya yi bayanin cewa bayanan sirrin da sojojin suka samu ne na cewa 'yan bindiga sun sace wasu mutane a gonarsu da ke kauyen Gwazunu, yasa suka bi sahu.

Ya kara da cewa jami'an tsaro da aka tura da gaggawa ne suka yi musayar wuta tsakaninsu da 'yan bindigar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel