Jihohi 19 sun amince da kudirin gwamnatin tarayya dna fasa jarabawar WAEC bana

Jihohi 19 sun amince da kudirin gwamnatin tarayya dna fasa jarabawar WAEC bana

Kwamishanonin ilimi na jihohi 19 dake Arewacin Najeriya sun bayyana amincewarsu da dakatad da shirin bude makarantu ga daliban azuzuwan karshe da gwamnatin tarayya tayi.

Kwamishanonin sun bayyana hakan ne a takardar da suka saki a Kaduna ranar Asabar bayan ganawar da sukayi ta yanar gizo inda suka tattauna yiwuwan bude makarantu da inganta bangaren ilimi.

Kwamishana ilimin jihar Kaduna, Dakta Shehu Makarfi, wanda shine shugaban kungiyar kwamishanonin ilimin Arewacin Najeriya ya rattaba hannu kan takardar, Punch ta samu.

Kwamishanonin jihohi goma sha uku (13) da suka samu halarta sune na Kaduna, Bauchi, Gombe, Niger, Nasarawa, Adamawa, Taraba, Kogi, Kwara, Katsina, Kano, Borno daJigawa.

Kwamishanonin sun yabawa ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, bisa yanke wannan shawara na hana bude makarantu kuma suna masu mara masa baya.

A cewarsu, cigaba da rufe makarantu saboda yadda cutar Korona ke cigaba da yaduwa shine mafita daya domin kare rayukan dalibai.

A cewarsu, "Mun yanke shawarar cewa ba za'a bude makarantu ba har sai an tabbatar komai ya daidaita kuma jihohi sun bi sharrudan kare kai da hukumar NCDC ta gindaya.

"Hakazalika ba zamuyi musharaka cikin jarrabawar WAEC da wasu jarabawowi ba har sai abubuwa sun daidaita bisa jagorancin ma'aikatar ilimin tarayya."

Jihohi 19 sun amince da kudirin gwamnatin tarayya dna fasa jarabawar WAEC bana
Jihohi 19 sun amince da kudirin gwamnatin tarayya dna fasa jarabawar WAEC bana
Asali: Depositphotos

Mun kawo muku rahoton cewa Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ya bayyana cewa daliban Najeriya da ke ajin karshe a makarantun sakandare ta gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC ba a bana.

Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Laraba bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC.

Ya kuma kara da cewa har yanzu ba a tsayar da ranar da za a bude makarantun ba a kasar kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Adamu ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da ke shirin bude makarantu su hakura su canja shawara saboda annobar korona.

"Ina kira ga gwamnatocin jihohi da suka amince za su bude makarantu su sake shawara saboda halin da muke ciki na annobar COVID-19. Ina ganin akwai hatsari cikin yin hakan. Mu kare yaran mu," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel