Hotunan hatsabiban ƴan bindiga da sojoji suka kashe a Arufu
Hedkwatan Tsaro ta Najeriya ta ce Dakarun Sojojin Najeriya karkashin “Operation Whirl Stroke” a ranar Juma'a sun yi nasarar kashe wasu gawurtattun Yan bindiga da suke adabar garuruwa a Benue da Taraba.
Kakakin Hedkwatan Tsaron, Manjo Janar John Enenche ya sanar a ranar Asabar cewa jajircewa da kwazon sojojin ne yasa suka samu nasara a jihohin biyu.
Enenche ya ce an kai sumamen ne bayan samun ingantattun bayanan sirri a ranar 10 ga watan Yuli cewa yan bindiga sun shigo garin Chambe a karamar hukumar Logo ta jihar Benue inda aka kashe mutum biyu.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Ba zan taɓa yin arziki ba muddin ina tare da shi - Matar aure ta garzaya kotu
Ya ce sojojin sun yi isa wurin da abin ya faru cikin gaggawa amma yan bindigan sun tsere kafin su iso.
A cewarsa, sojojin sun bi sahun yan bindigan zuwa wani karamin sansani da ke kusa da Arufu a jihar Taraba da ke makwabtaka da Benue.
"Da ganin sojojin, yan bindigan suka bude musu wuta amma sojojin sun yi galaba a kansu inda suka kashe guda biyu sannan saura suka tsere da rauni sakamakon harbin bindiga.
"A yayin artabun, sojojin sun kwato bindiga AK 47 guda daya da harsashi 7.62mm.
"Bugu da kari, jaruman sojojin sun mamaye garin suka gudanar da bincike daga Arufu zuwa Akwana don tabbatar da fatattakan bata gari a garin.
"Rundunar Sojin ta taya dakarun sojojin murna kan nasarar da suka samu ta kuma bukaci kada suyi kasa a gwiwa wurin cigaba da aikin kawar da bata gari a yankin na Arewa maso tsakiya a kasar," inji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng