Harin Damboa: Sojoji 35 sun mutu, 30 sun bata

Harin Damboa: Sojoji 35 sun mutu, 30 sun bata

'Yan ta'adan kungiyar ISWAP da suka ware daga Boko Haram sun kai wa wata tawagar sojoji harin kwantar bauna a kauyen Bulabulin da ke Damboa mai nisan kilomita 40 daga Maiduguri.

Da farko an ruwaito cewa sojoji 23 ne suka riga mu gidan gaskiya a harin kamar yadda Hum Angle ta ruwaito.

Wata majiya daga hukumomin tsaro ta shaidawa AFP cewa, "Mun rasa sojoji 35 a harin. Wasu 18 sun jikkata yayin da har yanzu akwai sojoji 30 da ba mu gansu ba. Ba a san abinda ya faru da su ba."

"An gano wasu sabbin gawarwaki a cikin daji yayin da tawagar ceto ta shiga don binciko wadanda ba a gansu ba, hakan yasa adadin wadanda suka mutu ya karu," a cewar majiyar.

Harin Damboa: Sojoji 35 sun mutu, 30 sun bata
Harin Damboa: Sojoji 35 sun mutu, 30 sun bata. Hoto daga Hum Angle
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Umar: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan sabon shugaban riko na EFCC

Wata majiyar ta sake tabbatar wa AFP sabon adadin sojojin da suka mutu.

"An gano gawarwakin sojoji 35 a lokacin da tawagar masu bincike suka duba wurin da aka kai harin. Akwai wasu 30 da ba a gansu ba. Ba a san ko suna da rai ko kuma sun mutu ba," in ji shi.

Ya ce 'yan ta'adan sun kona wata motar da ke iya taka nakiya sannan suka sace motocci masu dauke da bindiga takwas, bindigu da wasu kayayyakin sadarwa.

"Harin bazata ne. Yan taadan sun jeru a gefen titi suka boye cikin sunkuru sannan suka bude wa tawagar sojojin wuta a lokacin da suke wucewa. Suna dab da su yayin da suke harbin," in ji majiyar.

Hedkwatar Tsaro ta Najeriya cikin wata sanarwar da ta fitar ta tabbatar da afkuwar harin amma ta ce sojoji biyu kacal ne suka mutu yayin da wasu hudu suka jikkata.

Ta kuma ce an kashe yan ta'ada 17 yayin artabu tsakanin sojojin da yan taadan.

Rikicin a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya yi sanadin mutuwar mutane 36,000 kuma kimanin mutum miliyan biyu sun rasa muhallansu.

Tun a watan Afrilu, Manyan Dakarun Sojojin Najeriya sun koma yankin ta Arewa maso gabas tare da babban hafsan sojin kasa, Laftanat Janar Tukur Buratai yana jagoranci.

A watan Yuni, Buratai ya ruwaito cewa sojojin suna samun nasarori a yakin da suke yi da 'yan ta'adan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel