Jerin shahrarrun yan siyasa 10 da suka mutu sakamakon cutar Korona

Jerin shahrarrun yan siyasa 10 da suka mutu sakamakon cutar Korona

Kimanin watanni biyar da bullar cutar Coronavirus a Najeriya ranar 27 ga Febrairu, 2020, kimanin yan Najeriya 30,748 sun kamu, 12,546 sun samu waraka kuma 689 sun rigamu gidan gaskiya, bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC.

Cikin wadannan 689 da suka mutu, akwai manyan masu kudi, yan kasuwa, ma'aikatan gwamnati da shahrarrun yan siyasa.

Daily Trust ta tattare jerin manyan yan siyasa 10 da cutar ta kashe:

1. Abba Kyari

Abba Kyari, babban na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma shugaban ma'aikatan fadarsa ya kamu da cutar ranar 24 ga Maris bayan dawowarsa daga kasar Jamun.

Bayan fama da cutar, ya rasu ranar 17 ga Afrilu a asibitin First Cardiology Consultants dake Legas kuma aka birneshi a makabartar Gudu dake Abuja.

2. Adebayo Sikiru Osinowo

Sanata Adebayo Osinowa wanda ya wakilce mazabar Legas ta gabas ya mutu sakamakon cutar a asibtin First Cardiology Consultants, inda Abba Kyari ya cika.

Osinowo ya kwashe shekaru 16 a majalisar dokokin jihar Legas kafin shiga majalisar dattawa.

3. Abiola Ajimobi

Tsohon gwamnan na jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya mutu ranar 25 Yuni yana mai shekara 70. Ajimobi ya yi Sanata karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy AD a 2003, sannan ya yi gwamnan jihar tsakanin 2011 da 2019.

Bayan kare wa'adin gwamna ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Jerin shahrarrun yan siyasa 10 da suka mutu sakamakon cutar Korona
Jerin shahrarrun yan siyasa 10 da suka mutu sakamakon cutar Korona
Asali: Twitter

4. Suleiman Adamu

A ranar 30 ga Afrilu, Suleiman Adamu, dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya. Gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya tabbatar da cewa lallai ya mutu ne sakamkon cutar Korona.

5. Yan majalisar dokokin Borno biyu; Umar Audi Jauro da Wakil Bukar

Mambobin majalisar dokokin jihar Borno biyu, Umar Audi Jauro da Wakil Bukar, sun rasu sakamakon cutar a watan Mayu.

6. Shuaibu Danlami

Wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar Gombe, Shiaubu Danlami, ya rasu sakamakon cutar ranar 31 ga Mayu.

Mutuwar ya wajabta kulle ofishin sakataren gwamnatin jihar.

7. Wahab Adegbenro

Kwamishanan lafiyan jihar Ondo, Wahab Adegbenro ya mutu ranar 2 ga Yuli, 2020 sakamakon cutar Korona.

An birneshi bisa koyarwan addinin Musulunci.

8. Aminu Adisa Logun

Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Kwara, Aminu Adisa Logun, ya rasu ranar 7 ga Yuli bayan yan sa'o'i da samun sakamakon gwaji cewa ya kamu da cutar Coronavirus.

9. Tunde Buraimoh

An yi jana'izar dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazabar Kosofe II, Tunde Buraimoh, a makabartar Ikoyi a ranar Juma'a bayan Sallah.

An birne Buraimoh, wanda ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi, bisa koyarwan addinin Musulunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel