Mun gaji, ba zamu iya ba - Sojoji 356 sun ajiye aikin Soja

Mun gaji, ba zamu iya ba - Sojoji 356 sun ajiye aikin Soja

Da alamun abubuwa sun fara tabarbarewa matsalar rashin tsaro a kasar nan yayinda Sojojin Najeriya dari uku da hamsin da shida (356) suka ajiye aikin Soja bisa dalili na gajiya da aikin.

Rahoto daga Premium Times ya nuna cewa da yawa cikin Sojojin da sukayi murabus daga aikin Soja sun kasance wadanda ke yakin Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.

Akwai wasu kuma dake aiki a wasu yankunan daban.

A yanzu dai hukumar Sojin Najeriya na fuskantar barazana a dukkan yankunan Arewacin Najeriya.

Yayinda ake fama da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas, ana fama da yan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa maso yamma, sannan rikicin makiyaya da manoma a tsakiya.

Amma sabanin Soji 356 da sukayi murabus sakamakon gajiya da aiki, wasu 24 daban sun yi ritaya saboda son karbar sarauta a kauyukansu, jimillan Soji 380 kenan, majiyar PT ya bayyana.

KU KARANTA: Maimakon haska bidiyon karbar dalan Ganduje, da aikin da ka yiwa mutane ka haska - Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki

Mun gaji, ba zamu iya ba - Sojoji 356 sun ajiye aikin Soja
Mun gaji, ba zamu iya ba - Sojoji 356 sun ajiye aikin Soja
Asali: UGC

Wata majiya a gidan Soja ta bayyana cewa jikin Soji duk ya mutu fiye da kowani lokaci karkashin Buratai.

Majiyar tace: "Dalilin da yawancinsu suka bada shine gajiya da aiki, kuma haka na nuna cewa ran mutane ya fara fita ne saboda rashin ingantaccen shugabanci."

"Hakan na nuni ga cewa abubuwa sun tabarbare", wani jami'an Soja daban da ke da masaniya kan lamarin.

Wata majiya daban tace banda wadanda ke murabus daga aikin Soja bisa tsari, Sojoji da dama sun gudu daga aikin musamman wadanda ke yakin Boko Haram a Arewa masio gabas, cewar majiya dake faggen fama.

Za ku tuna cewa a lokuta da dama kwamandoji da Sojoji sun bayyana a bidiyo suna kuka kan rashin isassun kayayyakin aiki da makamai domin yakar yan ta'addan Boko Haram.

Misalin haka shine lokacin da tsohon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi, ya bayyana cikin wani bidiyo yana bayanin yadda yan Boko Haram sun fi su yawan makami.

Ba tare da bata lokaci ba aka tsoge Olusegun Adeniyi kuma aka maye gurbinsa da Farouq Yahaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel