An hana likitocin Najeriya 58 zuwa Birtaniya

An hana likitocin Najeriya 58 zuwa Birtaniya

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, NIS, ta hana wa wasu likitocin Najeriya 58 zuwa kasar Birtaniya wato UK.

A cewar kakakin hukumar ta NIS, Sunday James, likitocin sun gama shiri tsaf na barin kasar ta wani jirgi na musamman da zai tashi daga filin jirage na Murtala Mohammed da ke Ikeja, Legas.

James ya ce hukumar ta NIS tana da ikon hana mutane shigowa kasar ko hana su fita daga kasar.

An hana likitocin Najeriya 58 zuwa Birtaniya
An hana likitocin Najeriya 58 zuwa Birtaniya. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Har wa yau, ya ce biyu daga cikin likitocin suna da izinin tafiya wato Visa yayin da 56 cikinsu ba su da ita.

"Hukumar Kula da Fice ta Najeriya ta hana wasu likitocin Najeriya 58 da suka yi yunkurin tashi a jirgin sama zuwa kasar Birtaniya barin kasar a jirgi mai lamba ENT 550," in ji sanarwar.

"An hana likitocin 58 barin kasar ne bisa laakari da sashi na 31 karamin sashi na 2a da 2b da suka bawa Shugaban NIS karkashin Immigration Act 2015 hana duk wani dan Najeriya barin kasar karkashin kaidojin da suka cikin dokar.

"Jirgin da aka dako hayarsa zai dauki likitoci 42 ne zuwa bayar da horo amma kuma su 58 ne kuma cikinsu 2 kawai ke da izinin shiga Birtaniya, wannan ya sa aka hana su tafiya."

James ya ce idan da an bar su sun fita daga kasar, da can kasar da suka tafi ta taso keyar su sun dawo gida.

Ya ce, "Hukumar ta NIS da ke da alhakin kula da shige da fice a kasar ba za ta bari yan kasar ta masu ilimi da suka san dokokin shiga da fice su tafi wata kasa ba tare da izinin zuwa kasar ba."

"An yi hakan ne don kiyaye hana su shiga can kasar musamman a wannan lokaci na annobar korona kuma sun saba dokar gwamnatin tarayya na hana tafiya ila ga muhimman abubuwa da amincewar gwamnati.

"Hukumar Lafiya ba ta sanar da NIS game da tafiyar ba a hukumance. Jirgin ya koma Landan ba tare da likitocin ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel