COVID-19: Dukkan kwamishinoni sun killace kansu a Nasarawa

COVID-19: Dukkan kwamishinoni sun killace kansu a Nasarawa

Kwamishinan labarai, al'adu da yawon buɗe ido na jihar Nassarawa, Dogo Shammah ya ce dukkan ma'aikatan fadar gwamnan jihar za su killace kansu daga ranar Juma'a don kare kansu daga kamuwa daga Covid-19.

Mr Shammah ya shaidawa manema labarai a ranar Juma'a kwamishinonin sun yanke shawarar killace kansu be bayan Atoni Janar kuma kwamishinan Shari'a na jihar Abdulkareem Kana ya kamu da coronavirus.

NAN ta ruwaito cewa wata ƙwaƙwarar majiya a ranar Juma'a a Lafiya ta bayyana hakan zai faru hakan yasa aka tabbatar daga bakin Shammah.

COVID-19: Dukkan kwamishinoni sun killace kansu a Nasarawa
COVID-19: Dukkan kwamishinoni sun killace kansu a Nasarawa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Kwamishinan yace za su killace kansu ne tun daga yau Juma'a har zuwa lokacin da sakamakon gwajin da aka yi musu ya fito don sanin matsayinsu.

Ya ce an dauki matakin kariyar ne saboda Atoni Janar din ya halarci taron Majalisar Zartarwa ta Jiha, SEC, da gwamna Abdullahi Sule ya jagoranta a ranar 3 ga watan Yuli.

Shammah ya ce gwamnan jihar ne ya bayar da umurnin killacewar a kan shawarar mataimakin gwamna, Dr Emmanuel Akabe wanda kuma shine shugaban kwamitin yaki da Covid-19.

Kwamishinan ya yi kira ga mazauna jihar su kwantar da hankulan su amma su cigaba da bin sharuddan Kiyaye yaɗuwar annobar kamar bayar da tazara, saka takunkumin fuska d.s.

Kana ya tabbatar da cewa shima ya kamu da ƙwayar cutar ta korona a hirar wayar tarho da ta yi da NAN a ranar Alhamis.

Ya ce makon da ga gabata ya fara rashin lafiya da suka hada da mura, mutuwar jiki da ciwon moƙogoro.

Ya ce ya halin yanzu ya killace kansa kuma yana shan magungunan da likitoci suka bashi.

A halin yanzu fiye da mutum 200 ne suka kamu da ƙwayar cutar ta coronavirus a jihar ta Nasarawa kamar yadda NAN ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel