Kada a hana dalibai zana jarrabawar WAEC a bana - Majalisar Wakilai

Kada a hana dalibai zana jarrabawar WAEC a bana - Majalisar Wakilai

Majalisar wakilai ta yi magana game da shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke na haramtawa daliban kasar nan zana jarrabawa WAEC a bana saboda annobar korona.

Kamar yadda jaridar Daily Nigeran ta ruwaito, majalisar ta roki gwamnatin kasar da ta sauya wannan hukunci da ta zartar na hana dalibai zana jarrabawar kammala karatun sakandire a bana.

Majalisar cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin ilimi, Farfesa Julius Ihonvbere ya sanya wa hannu a ranar Juma'a, ya ce soke jarabawar zai zamo koma baya ga shimfidar tsare-tsare da dama da aka yi a kasar.

A cewar 'yan majalisar, gwamnatin tarayyar ta dauki wannan hukunci ba tare da ankarar da duk wadanda abin ya shafa da wuri ba, lamarin da suka ce zai janyo sauye-sauyen fasali da manufofi.

Zauren Majalisar Wakilai
Zauren Majalisar Wakilai
Asali: Twitter

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewar daliban ajin karshe da za su kammala karatun sakandire a bana, ba za su rubuta jarrabawar WAEC ba sakamakon cutar.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, shi ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Furucin ministan ne ya zo ne bayan halartar zaman majalisar zartarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Legit.ng ta ruwaito cewa, ministan ya kuma kara da cewa har yanzu ba a tsayar da ranar da za a bude makarantun ba a kasar.

Haka zalika ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da ke shirin bude makarantu su hakura su sauya shawara saboda yadda likafar annobar korona ke cigaba babu sassauci.

"Ina kira ga gwamnatocin jihohi da suka amince za su bude makarantu su sake shawara saboda halin da muke ciki na annobar COVID-19. Ina ganin akwai hatsari cikin yin hakan. Mu kare yaran mu," in ji shi.

KARANTA KUMA: Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta dubu 30 - NCDC

Ya ce dukkan makarantun da ke karkashin gwamnatin tarayya za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an tabbatar an ci galaba a kan cutar korona.

Ministan ya yi kira ga hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandire a Afirka ta Yamma, WAEC, da gwamnatocin jihohi su canja shawarar su ta bude makarantu don yin jarrabawar.

A cewar Adamu, Hukumar WAEC ba ta da ikon shar'anta wa makarantun Najeriya lokacin da za su bude.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel