Shugaban jam'iyyar APC ya koma PDP a jihar Ondo
- Jamiyyar APC mai mulki ta rasa daya daga ckin mambobinta a jihar Ondo inda ya koma PDP
- Samuel Olorunwa Ajayi, shugaban jamiyyar a karamar hukumar Ese Odo ya koma PDP a ranar Jumaa 10 ga watan Yuli
- Sai dai Ajayi bai bayyana dalilin da yasa ya fice ya koma jamiyyar adawar ta PDP ba
Samuel Olorunwa, Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Ese- Odo na jihar Ondo ya yi murabus daga jam'iyyar.
The Cable ta ruwaito cewa Olorunwa ya mika wasikar yin murabus dinsa a sakatariyar jamiyyar a ranar Jumaa kuma ya sanar da cewa ya shiga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Asali: UGC
DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)
Tsohon shuganban jam'iyyar ta APC na goyon bayan Agboola Ajayi, mataimakin gwamnan jihar Ondo da ya fice daga jam'iyyar APC ya koma PDP a baya bayan nan.
A halin yansu, Ajayi suna sa in sa da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu kuma ya nuna shaawar cewa zai fito takarar gwamna domin fafatawa da Akeredolu a zaben watan Oktoba.
Ku saurari karin bayani ...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng