Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Magu - Ministan shari'a

Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Magu - Ministan shari'a

A yau, Juma'a, ne ministan shari'a sannan babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da dakatar da Ibrahin Magu, mukaddashin shugaban EFCC.

A cikin wani jawabi da kakakinsa, Umar Gwandu, ya fitar, Malami ya ce shugaba Buhari ya dakatar da Magu ne domin bawa kwamitin binciken da aka kama damar yin aikinsu ba tare da wani katsalandan ba.

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin darektan gudanarwa a hukumar EFFC, Mohammed Umar, a matsayin shugaban riko na hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a kammala bincike da sanar da mataki na gaba," a cewar sanarwar.

Legit.ng ta wallafa cewa jam'iyyar PDP ta bukaci a gurfanar da Magu bayan dakatar da shi domin tuhumarsa da aikata almundahana.

PDP ta bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da sakatarenta na watsa labarai, Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, a Abuja.

A cewar PDP, ta bukaci a gurfanar da Magu ne bayan nazarin dalilan da su ka sa har shugaban kasa ya kafa kwamitin bincike a kansa.

Jam'iyyar ta bayyana cewa binciken da ake gudanarwa a kan Magu ya tabbatar da zargin da ta dade ta na yi a kan cewa hukumar EFCC ta na rufawa jami'an gwamnati mai ci aisri tare da tozarta mambobin jam'iyyun adawa.

Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Magu - Ministan shari'a
Ibrahim Magu
Asali: UGC

A cewar Ologbondiyan; "bankado yadda Magu ya dinga sayar da kadarorin da EFCC ta kwace kamar yadda ministan Shari'a ya bayyana a cikin takardar korafi da kuma rahoton da ofishin hukumar DSS ya fitar, sun tona asirin irin cin mutunci da gwamnatin jam'iyyar APC ta yi wa wasu 'yan Najeriya da sunan yaki da cin hanci.

DUBA WANNAN: 'Yan arewa sun shawarci Buhari a kan mutumin da ya dace ya nada don maye gurbin Magu matukar ya na son ganin aiki da cikawa

"Abubuwan da su ka fito fili yanzu sun kara haskaka dalilan da suka sa yaki da cin hanci ya kara tabarbarewa a karkashin mulkin Buhari, kamar yadda sahihan kungiyoyin kasa da kasa suka nuna a cikin rahotanninsu.

"Ba kankanin abin kunya bane ga Najeriya a samu shugaban hukumar yaki da cin hanci da laifin aikata almundahana tare da barnatar da dukiyar da aka kwace domin mayarwa hannun gwamnati.

"Tunda yanzu asirinsa ya tonu, bai kamata shugaba Buhari ya ke kokarin nemawa Magu sassauci ko hana a gurfanar da shi a gaban kotu ba," in ji Ologbondiyan.

Magu, wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dakatar da shi, ya na fuskantar tuhume - tuhume ma su nasaba da almundahana da kama karya da sharara karya a gudanar da aikinsa na yaki da cin hanci da rashawa.

A ranar Litinin ne Magu ya fara bayyana a gaban kwamitin bincikensa da aka kafa a fadar shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel