Magu: Abdulsalami ya yi ƙarin haske a kan sumamen jami'an EFCC

Magu: Abdulsalami ya yi ƙarin haske a kan sumamen jami'an EFCC

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar a ranar Alhamis ya yi karin haske game da rubutun da tsohon kakakin marigayi shugaban kasa Umaru Yar’adua, Segun Adeniyi ya yi inda ya ce Magu ya aika da jami'an EFCC suyi bincike a gidan Abdulsalami da ke Minna a Niger.

Rubutun ra'ayin da ya wallafa ya janyo cece kuce a kafafan watsa labarai da na sada zumunta a cikin yan kwanakin nan.

Adeniyi ya yi hasashen cewa halin da Magu ya shiga a yanzu ba zai rasa nasaba da wasu azarbabin da ya yi yayin gudanar da aikinsa ba da suka hada da taba wasu manyan mutane a kasar.

EFCC sun ziyarci gida na cikin kuskure ne Abdulsalami
EFCC sun ziyarci gida na cikin kuskure ne Abdulsalami
Asali: UGC

Sai dai, sanarwar da Kakakin Abdulsalami, Kyaftin J. Mfon mai murabus ya fitar a kan batun ya nuna ba haka zance ya ke ba, ya ce hasali babu wata hukumar tsaro da ta taba bincikar gidan Abdulsalami.

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Ya ce, "An janyo hankalin mai girma Janar A Abubakar kan wata rahoto da ke cewa EFCC sun bincika gidansa da ke Minna, jihar Niger bisa umurnin mukadashin shugaban hukumar Ibrahim Magu, kuma yana son ya bayyana gaskiyar abinda ya faru.

"EFCC ko wata hukumar tsaro ba ta taba zuwa gidansa ta yi bincike ba.

"Sai dai a shekarar 2017, wasu jamian hukumar daga Kano sun tafi Minna suna neman wani gida a Tunga. Tawagar sun isa gidan hutawar Abdulsalami da ke Minna suka fadawa masu tsaron gidan cewa an aiko su su bincika gidan.

"Jamian sun ce kuskure ne suka yi duba da cewa akwai rudani kan yadda lambobin gidaje suke a Tunga. Da aka tuntubi Magu, ya ce bai san da labarin zuwa binciken gidan ba. Daga nan jamian na EFCC suka koma Kano.

"Abinda mai girma ya fahimta shine sun tafi gidansa ne a kan kuskure. Amma ba su shiga ba ballanta su bincika gidan.

"Hasali ma, Mai Girma baya tsokaci a kan rubuce rubucen da ake yi game da shi a jaridu. Ya dauki matakin yin martani a kan wannan ne saboda irin cece kuce da batun ya janyo.

"Mai Girma ya ga akwai bukatar ya yi wannan bayanin mai muhimmanci sakamakon hasashen da wasu ke yi a kafafen watsa labarai cewa akwai hannunsa cikin abinda ke faruwa da Magu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel