Kawai ana kokarin bata min suna ne - Magu kan rahoton cewa ya baiwa VP Osinbajo N4bn

Kawai ana kokarin bata min suna ne - Magu kan rahoton cewa ya baiwa VP Osinbajo N4bn

- Zargin amsan N4bn hudu daga hannun Magu, Osinbajo ya kai kara wajen IG na yan sanda

- Manyan Diraktocin EFCC 16 sun gurfana gaban kwamitin bincike

- Lauyan Magu sun bukaci a bashi beli

Mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, Ibrahim Magu, ya karyata rahotannin da ke cewa ya baiwa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, kudi N4bn.

Ya karyata rahoton ne yayinda ya gurfana gaban kwamitin bincike da fadar shugaban kasa ta shirya karo na hudu ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, 2020.

Majiyar The Nation ta ruwaito Magu da cewa ko kadan bai fadawa kwamitin ya baiwa mataimakin shugaban kasa N4bn ba.

Ya ce ta ina zai samu irin wadannan kudaden da zai iya baiwa wani? Kawai ana son bata masa suna ne.

A cewar Majiyar, Magu yace: "Ban fadawa kwamitin cewa na baiwa mataimakin shugaban kasa N4 billion ba."

"A ina zan samu irin wadannan kudaden? Ta ina zan ga irin wannan kudi? Kawai duk cikin kokarin bata min suna ne."

"Bani da iko kan irin wadannan kudaden, ban bada umurnin baiwa mataimakin shugaban kasa ko wani N4 billion ba."

"Ko kadan ba'a ambaci sunan mataimakin shugaban kasa a tattaunawar kwamitin binciken ba. Kuma tunda ba'a ambaceshi ba, ta yaya zan yi maganar cewa na bashi N4bn."

Ban baiwa VP Osinbajo N4bn ba - Ibrahim Magu
Ban baiwa VP Osinbajo N4bn ba - Ibrahim Magu
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwana 4 a tsare: Ibrahim Magu ya bukaci a basa beli ya tafi gida

Legit ta kawo muku rahoto ranar Alhamis cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai kara wajen Sifeto Janar na yan sanda kan jawabin kafar sadarwar Tuwita da ta zargesa da amsan N4bn daga hannun Magu.

Ya bukaci IG na yan sanda ya gudanar da bincike kan lamarin.

A cikin wasikar da Osinbajo ya rubutawa IGP ranar Laraba ta hannun lauyansa, Taiwo Osipitan, ya bayyana rahoton a matsayin kage da sharri domin bata ma sa suna, a saboda haka ya bukaci a bi ma sa hakkinsa.

Kazalika, Osinbajo ya aika kwafin wasikar zuwa ofishin ministan shari'a, Abubakar Malami.

Wata kafar yada labarai ta yanar gizo, PointBlank, mallakar Jack Ude, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta wallafa rahoton cewa Magu ya barnatar da biliyan N39 tare da bawa Osinbajo biliyan N4 daga cikin kudin a matsayin toshiyar baki.

Rahoton ya yi ikirarin cewa wata majiya ce daga cikin kwamitin binciken Magu ta sanar da jaridar labarin bawa Osinbajo kudin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel