Yanzu-yanzu: An yi jana'izar dan majalisar Legas, Tunde Buraimoh

Yanzu-yanzu: An yi jana'izar dan majalisar Legas, Tunde Buraimoh

An yi jana'izar dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazabar Kosofe II, Tunde Buraimoh, a makabartar Ikoyi a ranar Juma'a bayan Sallah.

An birne Buraimoh, wanda ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi, bisa koyarwan addinin Musulunci.

Ya mutu yana mai shekaru 60.

An samu labarin cewa marigayi Buraimoh, wanda shine Kakakin majalisar ya kwashe makonni biyu bai zuwa zauren Majlisa.

Hakazalika rahotanni sun bayyana cewa ya rasu bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC na jihar Legas, Tunde Balogun yace: "Akwai takaici. Babban rashi ne ga jam'iyyar mu, iyalansa, jihar Legas da Najeriya gaba daya."

Da safiyan nan mun kawo muku rahoton cewa dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar mazabar Kosofe II, Hanarabul Tunde Buraimoh, ya rigamu gidan gaskiya.

Takwaransa dake wakiltar mazabar Kosofe I, Sanni Ganeey Okanlawon, ya tabbatar da hakan a shafin na Facebook inda yace "Wannan abu yayi yawa, Ka huta Tunde Buraimoh."

Yanzu-yanzu: Wani dan majalisa daga Legas ya mutu
Yanzu-yanzu: Wani dan majalisa daga Legas ya mutu
Asali: Twitter

KU KARANTA: An janye dogaran Ibrahim Magu gaba daya, an canja musu wajen aiki

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel