Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai rattafa hannu kan gyararren kasafin kudin 2020 gobe Juma'a

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai rattafa hannu kan gyararren kasafin kudin 2020 gobe Juma'a

Shugaba kasa, Muhammadu Buhari, zai rattafa hannu kan gyararren kasafin kudin 2020 da ya aika majalisar dokokin tarayya a gobe Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2020.

Hadimin Buhari kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan da yammacin Alhamis a shafinsa na Tuwita.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai rattafa hannu kan gyararren kasafin kudin 2020 gobe Juma'a
Credit: Presidency
Source: Twitter

Kwanaki 29 da suka gabata, Majalisar wakilan kasar nan ta amince da gyararren kasafin kudin 2020 inda ta kara shi daga N10.5 tiriliyan zuwa N10.8 tiriliyan.

Duk da cewa kwamitin kula da kasafin kudin wanda rahotonsu aka yi amfani da shi a majalisar a ranar Laraba, sun bukaci a yi amfani da N10,801,544,664,642.

'Yan majalisar sun kara da naira biliyan hudu na walwalar kungiyar likitoci masu neman kwarewa bayan barazanar yajin aiki da suka yi.

Hakazalika, majalisar ta amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aro kudi har dala biliyan 5.513 don amfanin kasar nan.

Bugu da kari, Gwamnatin tarayya ta sanya takunkunmi kan daukan aikin yi a ma'aikatun gwamnatin tarayya gaba daya.

Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana hakan ne yayinda take hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba.

Ta ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan ma'aikata albashi kuma ba zata sallami ma'aikata ba amma ba za'a sake daukan sabbin ma'aikata ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel