Hushpuppi: Dubai ta tsame 'yan Najeriya daga neman aiki tare da samun Visar shakatawa

Hushpuppi: Dubai ta tsame 'yan Najeriya daga neman aiki tare da samun Visar shakatawa

- Bayan damke Hushpuppi, wasu kamfanoni a Dubai sun fara tsame 'yan Najeriya daga cikin wadanda za su iya samun aiki a wurinsu

- Baya ga tsame 'yan Najeriya daga wadanda za su bai wa aiki, sun haramta bai wa 'yan Najeriya Visar shakatawa

- Idan za mu tuna, 'yan sandan Dubai da suka kama Hushpuppi, sun mika shi Amurka a kan zargin damfara

Kamfanoni a Dubai sun fara tsame 'yan Najeriya daga cikin jerin mutanen da za su dauka aiki bayan da 'yan sanda suka kama Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi a daular larabawan.

Idan za mu tuna, an damke Hushpuppi da wasu 'yan Najeriya a kan damfara a Dubai tare da mika su Amurka.

Legit.ng ta ga tallan wasu ayyyuka a yanar gizo a kasar Dubai inda aka bayyana cewa banda 'yan Najeriya a wadanda suke bukata.

Bayan nan, an fara hana 'yan Najeriya Visa zuwa yawon bude ido a kasar.

A wasikar da Legit.ng ta gani, kasar ta sanar da 'yan Najeriya masu fasfotinta cewa, bata amince su samu hatimin shiga kasar ba don yawon bude ido na wannan lokacin.

"Mun gode da ku ka tuntubemu. Amma muna takaicin sanar da ku cewa ba a amince ba saboda duk 'yan Najeriya da ke da fasfotin kasar, ba a aminta da basu damar shiga UAE ba don yawon bude ido.

"Amma kuma, akwai yuwuwar hakan ta sauya a kowanne lokaci," wasikar tace.

KU KARANTA: Dumu-dumu: Yadda aka kama wani fitaccen shugaba a APC yana lalata da kananan yara

A wanai labari, a makonni kalilan da suka gabata, 'yan sanda a Dubai sun damke wani mai dukiya a Najeriya mai suna Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Daga bisani sun mika shi kasar Amurka inda aka damke shi a hannun 'yan sandan kasar.

A halin yanzu, Hushpuppi na tsare a gidan gyaran hali na birni da ke Chicago.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto cewa akawun dinsa na Google ne ya yi sanadiyyar da aka kama Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.

An yi ram da Hushpuppi ne a garin Dubai kwanaki, daga nan jami’an kasar Amurka su ka yi nasarar dauke shi daga UAE domin ya amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su.

Ana zargin Hushpuppi a gaban wani kotun Amurka da laifin wawurar dukiyar mutane ta hanyar damfara da zamba cikin aminci.

A wasu takardu da su ka shigo hannun The Cable, an gano cewa jami’an FBI sun yi nasarar gano inda Hushpuppi ya ke ne bayan ya aika sako ta yanar gizo da wata wayarsa ta iPhone.

Ma’aikatan hukumar FBI da ke bincike a Amurka sun gano cewa Hushpuppi ya nemi a turo masa wasu kudi zuwa wani asusunsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel