Modo Sheriff ya kai ziyarar bazata sakatariyar APC da ke Abuja

Modo Sheriff ya kai ziyarar bazata sakatariyar APC da ke Abuja

- Jigo a jamiyyar APC, Sanata Ali Modu Sherrif ya kai ziyara sakatariyar jam'iyyar ta kasa da ke birin tarayya Abuja

- Rahotanni sun ce ya shiga cikin sakatariyar na dan mintoci sannan ya fito ya shiga motarsa ya tafi ba tare a ya yi magana da 'yan jarida ba

- Masu nazarin al'amuran siyasa na hasashen cewa ziyarar ta Ali Modu Sheriff ba za ta rasa nasaba da neman kujerar shugabancin jam'iyyar ba

Tsohon shugaban jamiyyar PDP kuma a yanzu jigo a jam'iyyar APC, Sanata Ali Modu Sheriff a ranar Alhamis ya kai ziyarar bazata zuwa hedkwatan APC na kasa da ke Abuja.

Rahotanni sun ce an tuka Sheriff zuwa hedkwatan jam'iyyar cikin wata bakar G-wagon misalin karfe 4.15 na yamma kuma ya shiga ya gana wasu 'yan kwamitin riko.

Ya fito daga hedkwatan bayan wasu 'yan mintuna amma bai amsa tambayoyin da manema labarai suka yi masa ba.

Modo Sheriff ya kai ziyarar bazata hedkwatar APC
Ali Modu Sherriff. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Duk da cewa ba a tabbatar da dalilin ziyararsa ba zuwa hedkwatan ta APC, ana rade radin cewa yana neman kamun kafa ne kan iko da jami'yyar musamman a yankin Aewa maso Gabas.

The Nation ta ruwaito cewa wata kwakwarar majiya daga ofishin shugaban kwamitin rikon ta ce shugabanin biyu za su bar hedkwatan jami'yyar ne zuwa wani wuri na sirri da za su gana.

Sherrif ya yi gwamna a jihar Borno na waddi biyu sannan ya tafi majalisar dattijai a matsayin sanata.

Yana daya daga cikin wadanda aka kafa jami'yyar APC da su amma ya fice daga jamiyyar saboda rashin jituwa tsakaninsa da Kashim Shettima da wasu shugabanin APC na kasa.

Ana sa ran kwamitin riko karkashin jagorancin gwamnan Yobe, Mai Mala Buni za ta gudanar da gangamin taron jamiyyar na wannan shekarar.

Wasu masu nazarin al'amuran siyasa a kasar sun ce Modu Sheriff, Sanata Kashim Shettima da tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Legas, Janar Buba Marwa (mai ritaya) suna daga cikin masu neman kujerar shugabancin jamiyyar ta APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel