Abubuwa 7 da suka faru da dakataccen shugaban EFCC Ibrahim Magu

Abubuwa 7 da suka faru da dakataccen shugaban EFCC Ibrahim Magu

Cikin yan kwanaki 12 fari daga ranar Litnin 6 ga watan Yuli, 2020 zuwa yau Asabar, 18 ga Yuli, 2020, muhimman abubuwa 7 sun faru da shirin yaki da cin hanci da rashawan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

A lokutan yakin neman zabe na shekarar 2015 da 2019, shugaba Muhammadu Buhari bai gushe ba, yana jaddada cewa yakin cin hanci da rashawa na cikin abubuwa uku mafi muhimmanci da zai yi.

Amma da alamun wanda ya nada don wanzar masa da wannan manufa na cikin halin kakanikaye kuma yakin da rashawar na fuskantar barazana.

KU KARANTA: Shin wanene ainihin wanda aka nada rikon kwayar kujerar Magu?

Legit ta tattaro muku jerin abubuwa 7 da suka faru da dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

1. An kamashi ranar Litinin

A ranar Litinin 6 ga Yuli, 2020, wasu jami'an tsaro sanye da farin kaya sun tsare Ibrahim Magu yayinda yake kokarin zuwa ofishin sifeton yan sanda IG Mohammed Adamu.

Sun tare shi a bakin kofa kuma sukayi awon gaba dashi zuwa fadar shugaban kasa.

2. Ya gurfana gaban kwamitin bincike na musamman karkashin Alkali Ayo Isa Salami

Yayinda jami'an tsaron suka dira da shi fadar shugaban kasa, Magu ya gamu da wata kwamiti na musamman da shugaba Muhammadu Buhari ya nada domin yi masa tambayoyi.

Kwamitin karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun kolin Najeriya, Alkali Ayo Isah Salami, ta na da hakkin yi masa tambayoyi kan wasu tuhume-tuhume da ake yi masa.

KARANTA NAN: Jerin tuhume-tuhume 10 da ake yiwa shugaban EFCC, Ibrahim Magu

3. A tsareshi a ofishin yan sanda

A misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ta kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami'an yan sandan sun yi awon gaba da shi.

An dakatad da dogaransa kafin aka iya tafiya da shi.

The Nation ta samu labarin cewa bayan zaman tambayoyin da akayi masa, an shigar da Magu wata motar fara kirar Hilux mai lamba 37ID.

Amma Magu ya ce sam ba zai shiga ciki ba, sai dai ya zauna a bayan motar. Daga baya yan sandan suka shawo kansa ya shiga cikin motar.

Daga karshe dai aka garzaya dashi ofishin binciken hukumar yan sanda FCID cikin motarsa.

4. An dakatad da shi daga kujerarsa

A ranar Talata, Mininstan SHari'a, Abubakar Malami, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya dakatad da Ibrahim Magu matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC kuma an nada Mohammed Umar matsayin shugaban rikon kwarya.

5. Kai simame tare da birkice gidajensa

Wasu jami'an 'yan sanda da ke aiki da sashen binciken manyan laifuka (FCIID) sun birkice gidan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaba Buhari ya dakatar.

Wani babban jami'in dan sanda ya tabbatarwa da jaridar 'Punch' cewa an gudanar da bincike a gidan Magu da ke kan titin Abduljalil a unguwar Karu da ke wajen birnin tarayya, Abuja.

Babban jami'in ya bayyana cewa sun kwashe wasu muhimman takardu daga gidan Magu bayan sun shafe sa'o'i su na gudanar da bincike.

6. Ya koma kwana Masallaci a Garki

A ranar 11 ga watan Yuli, Wani rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa Ibrahim Magu, ya daina kwana cikin ofishin yan sanda kamar yadda yayi kwanaki hudun farko da aka tsareshi.

Ya koma kwana a Masallacin dake cikin hedkwatar hukumar FCID.

7. An sake Magu bayan kwanaki 9 a tsare

An sake Magu ranar Laraba, 15 ga Yuli, 2020 bayan kai komon da Lauyansa, Wahab Shittu, ya rika yi tsakanin fadar shugaban kasa da ofishin sifeto janar na yan sadan.

A farko kwamitin tace IG na yan sanda ke tsare Magu, amma daga baya IG yace ba shi ke rike Magu ba. Daga karshe Lauyan ya karbi belinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel