Kano: Ganduje ya nada Salihi a matsayin shugaban KIRS

Kano: Ganduje ya nada Salihi a matsayin shugaban KIRS

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Abdurrazak Datti Salihi a matsayin Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta jihar Kano, KIRS.

Salihi ya karbi ragamar mulkin hukumar daga hannun Muhammad Inuwa, wanda aka nada a matsayin shugaban wucin gadi na tsawon watanni hudu.

Ganduje ya mika godiyarsa tare da yabawa kokarin Inuwa yayin jagorancin da ya yi na riko kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kano: Ganduje ya nada Salihi a matsayin shugaban IRS
Kano: Ganduje ya nada Salihi a matsayin shugaban IRS
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce, "Mun yi farin ciki da irin kokari da jajircewa ta Inuwa a KIRS. A matsayinsa na shugaban riko, ya yi jagoranci mai kyau tun daga watan Maris da aka nada shi zuwa yanzu."

Inuwa zai cigaba da kasancewa shugaban hukumar samar da kayan aikin noma na jihar Kano, KASCO, matsayin da ya ke rike da ita lokacin da ya ke jagorancin KIRS.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya amince da fitar da N108bn don ginin titi a jihohi hudu

Ganduje cikin sanarwar da sakataren watsa labaransa, Abba Anwar ya fitar ya ce nadin da aka yi wa Salihi zai fara aiki nan take.

Sabon shugaban na KIRS (Salihi) kwararren Akanta ne. An gano cewar ya shafe kimanin shekara 20 yana aiki a bangaren kudi a banki da kamfanoni masu zaman kansu.

Kafin nadinsa, Salihi ne shugaban Hukumar SIFMIS a Ma'aikatar Kudi ta Jihar Kano ya kuma rike mukamin Direktan Harajin PIT a Hukumar Karbar Haraji ta Jihar Kano.

Ya kuma rike mukamin Shugaban Bangaren Kudi a Bankin Manoma, BoA, ta Jihar Kano. Ya kuma rike mukamin Shugaba a Bankin Tallafawa Manoma da Cigaban Karkara, NACRDB, a Jihar Sokoto da dai wasu mukaman.

Gwamna Ganduje ya bukaci sabon shugaban na KIRS ya yi aiki takuru kana ya jawa ma'aikatansa kusa suyi aiki tare domin cigabar ma'aikatar da jihar Kano baki daya.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Ganduje ya aika wa Majalisar Jihar sunayen kwamishinoni uku da ya zaba domin samun amincewar majalisar.

Kakakin Majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Talata a Kano kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Gafasa ya ce gwamnan na neman amincewar majalisar domin nada Idris Garba a matsayin kwamishina kuma mamba na Majalisar Zartarwa na Jihar, SEC.

Ya ce gwamnan ya kuma nemi yan majalisar su tabbatar da nadin wasu kwamishinoni biyu a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na jihar, KANSIEC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel