Kebbi: 'Yan bindiga sun kashe hakimi
'Yan bindiga sun kashe hakimin garin Bajida da ke karamar hukumar Fakai ta jihar Kebbi, Alhaji Musa Muhammad Bahago, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Yayan hakimin da aka kashe, Alhaji Umar Muhammad, ya yi bayanin cewa an kashe kaninsa a ranar Laraba tsakanin karfe 4 zuwa 6 na yamma a yayin da yake kan hanyar komawa gidansa da ke garin Zuru.
"Ya rasu yana da shekaru 56 kuma ya bar mata hudu da 'ya'ya masu tarin yawa," Muhammad yace.
A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Nafi'u Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Ya ce: "Da gaske ne kuma mun san da aukuwar lamarin mai cike da takaici."
Ya kara da bayanin cewa: "Yana tuki don isa gida daga Zuru amma sai 'yan bindiga suka biyo shi tare da kashe shi.
"Muna kokarin ganin mun damko masu mugun aikin don su fuskanci hukuncin da ya dace."
KU KARANTA: Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba
A wani labari na daban, kamar yadda rahoto daga kauyen 'yar Gamji na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ya bayyana, wasu 'yan bindiga 200 dauke da miyagun makamai sun kai hari tare da kashe mutane sama da 15.
'Yan bindigar da suka tsinkayi kauyen a kan babura, sun halaka manoman da suka samu a gona.
'Yan bindigar sun isa kauyen wurin karfe 10 na safe kuma sun yi ruwan wuta na a kalla sa'a daya, mazauna yankin suka sanar da Daily Trust.
"Bayan 'yan bindigar sun gama ruwan wuta, mun je inda muka dauke gawawwakin. Mun kirga gawawwaki 15," daya daga cikin mazauna kauyen ya sanar duk da ya bukaci a sakaya sunansa.
Ya sanar da cewa a yau za a birne mamatan. Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda 'yan bindigar suka isa kauyen 'Yar Gamji wanda ke kan titin Katsina zuwa Dutsinma zuwa Kankara zuwa Funtua. Yana da nisan kilomita a kalla 30 daga cikin garin Katsina.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng