Kwastam ta kama buhunan shinkafa 140 da aka ɓoye cikin yashi

Kwastam ta kama buhunan shinkafa 140 da aka ɓoye cikin yashi

Rundunar hadin gwiwa na yaki da masu fasakwabri na musamman ta gwamnatin tarayya, JBOD, ta kama wata babban mota dauke da buhunnan shinkafan kasasashen waje 140 da aka boye a cikin yashi.

Tawagar da ke kula da jihohin Arewa maso Tsakiya na Niger, Kwara, Kogi da Benue sun tare wata mota mai lamba ZAR 803 XA, a garin Kontagora da ke jihar Niger.

Shugaban tawagar, Mohammed Garba, a ranar Laraba a Ilorin ya ce, Hedkwatan rundunar da ke jihar Kwara ta ce shinkafar da aka kama ya kai ta N2,142,000.

Kwastam ta kama buhunan shinkafa 140 da aka boye cikin kasa
Hameed Ali. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Ya kara da cewa a cikin kwanaki arbain da suka shude, JBOD ta kama kayan da suka samar da kudaden shiga na N1,207, 223, 380 yayin da an kama wadanda ake zargi da laifuka 53.

Ya ce, "Ina son ku mika wa makiya tattalin arzikin Najeriya wannan sakon cewa hukumar ta inganta dabarun ta na yaki da masu shigo da shinkafar kasashen waje da wasu kayayyakin ta haramtattun hanyoyi.

"Sabbin dabarun da kasashen duniya ke amfani da su wurin dakile fasakwabri da muke amfani da su tare da taimakon tawagar da ke kula da mu karkashin jagorancin Kwantrola Janar, Hameed Ibrahim Ali (ritaya) ta bamu ikon samun nasarorin nan."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Rundunar 'Yan sanda sun kama wani Francis Diamond da ake yi wa lakabi da Iron Man, shugaban wata mugunyar kungiyar asiri ta Aiye a jihar Legas.

An kama Diamond ne bayan wasu hare hare da kisar kai da fashi da makami da aka yi a unguwanin Ajah da Epe a jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Legas ta danganta laifukan da aka aikata da kungiyar asirin ta wanda ake zargin.

Yan sandan sun kuma kama wasu mambobin kungiyar takwas a sassa daban na Ikorodu bayan shugaban kungiyar ya bayyana musu inda suke.

An ce wadanda ake zargin sun kashe wani dan kungiyar da suke kishi a Odonguyan, Ikorodu kuma suka kai wa wasu mutane a yankin hari.

'Yan sandan sun ce Diamond ya amsa cewa ya dauki faifan bidiyon lokacin da ake kashe dayan dan kungiyar da suke adawa da adda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel