Dumu-dumu: Yadda aka kama wani fitaccen shugaba a APC yana lalata da kananan yara

Dumu-dumu: Yadda aka kama wani fitaccen shugaba a APC yana lalata da kananan yara

Wani dan siyasa mai suna Christopher Ogah ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa a karamar hukumar Obi ta jihar.

An kama dan siyasar yana yi wa yara mata biyu fyade a gidansa da ke karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

Wani ganau ba jiyau ba, mai suna Oyikobi Ambasada, ya ce dan siyasar shine shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Obi.

Ya ce yaran mata suna da shekaru 12 da 13, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Wata majiya wacce ta bukaci a sakayata, ta ce dan siyasar ya ja yaran mata kanana ne bayan da suka shiga gidansa diban ruwa a rijiya.

Majiyar ta bayyana cewa, wannan ba shine karo na farko ba da aka kama shugaban jam'iyyar APC yana aikata wannan aika-aikar ba.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Mohammed Oyimoga Oyigye, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce da kan shi ya kwace wanda ake zargin daga hannun jama'ar da suka yi yunkurin banka mishi wuta sannan ya mika shi hannun 'yan sanda.

An mayar da wanda ake zargin zuwa garin Lafia don gujewa karantsaye ga zaman lafiyar da ke yankin.

A martanin kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe, ya ce, "Na bada umarnin mika al'amarin gaban sashen bincike na musamman da ke lafiya. Bayan kammala bincike, za a mika shi gaban kotu.

Dumu-dumu: Yadda aka kama wani fitaccen shugaba a APC yana lalata da kananan yara
Dumu-dumu: Yadda aka kama wani fitaccen shugaba a APC yana lalata da kananan yara. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun damke mata biyu da suka birne jaririya da ranta a Kaduna

"Jami'an 'yan sanda na jan kunnen masu fyade da su sauya hali ko su fuskanci fushin hukuma.

"Ina tabbatar wa da jama'a cewa rundunar 'yan sandan za ta kama tare da gurfanar da duk wanda ta ga ta dace komai matsayinsa."

A wani labari na daban, 'yan sanda a jihar Ogun sun kama wani faston cocin Christ Apostolic Church (CAC) a yankin Ogo Oluwa, mai suna Oluwafemi Oyebola da ake zargi da yi wa yar cikinsa fyade.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama faston ne bayan 'yarsa ta shigar da rahoto a hedkwatar 'yan sanda da ke Owode-Egbado.

Sanarwar da kakakin 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ta fitar ya bayyana cewa yarinyar ta ce mahaifinta ya fara tilasta mata yin lalata da shi ne tun shekarar 2015 a lokacin shekarun ta 19 jim kadan bayan rasuwar mahaifiyarta.

A cewar ta, sau uku mahaifin nata yana yi mata ciki kuma yana kai ta wurin wata maaikacciyar asibiti ana zubar da cikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel