'Yan sanda sun kama hatsabibin shugaban kungiyar asiri da mambobinsa 8

'Yan sanda sun kama hatsabibin shugaban kungiyar asiri da mambobinsa 8

Rundunar 'Yan sanda sun kama wani Francis Diamond da ake yi wa lakabi da Iron Man, shugaban wata mugunyar kungiyar asiri ta Aiye a jihar Legas.

An kama Diamond ne bayan wasu hare hare da kisar kai da fashi da makami da aka yi a unguwanin Ajah da Epe a jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Legas ta danganta laifukan da aka aikata da kungiyar asirin ta wanda ake zargin.

Yan sandan sun kuma kama wasu mambobin kungiyar takwas a sassa daban na Ikorodu bayan shugaban kungiyar ya bayyana musu inda suke.

'Yan sanda sun kama hatsabibin shugaban kungiyar asiri da mambobinsa 8
'Yan sanda sun kama hatsabibin shugaban kungiyar asiri da mambobinsa 8. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

An ce wadanda ake zargin sun kashe wani dan kungiyar da suke kishi a Odonguyan, Ikorodu kuma suka kai wa wasu mutane a yankin hari.

'Yan sandan sun ce Diamond ya amsa cewa ya dauki faifan bidiyon lokacin da ake kashe dayan dan kungiyar da suke adawa da adda.

Shugaban kungiyar ya ce, "Na daura bidiyon a intanet saboda kowa ya gani musamman 'yan kungiyarsa. Shi ne ya tsara wata harin da aka kai wa dan kungiyar mu."

Kakakin rundunar yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya bayar da sunayen 'yan kungiyar da aka kama kamar haka;

Olaitan Apampa; Chidi Michael, 25; Eno Sunday, 25; Saheed Gbadebo, 23; Adepeju Azeez, 38; Samuel Ilesanmi; Omotosho Quadri, 25, da Moses Ogungbe, 28.

Elkana ya ce binciken da yan sanda suka gudanar ya nuna cewa Apampa ne ya harbi wanda suka kashe bayan sun gama sararsa da adda.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce, "Wadanda ake zargi yan kungiyar asiri ta Eiye ne. Sun ce sun kashe matashin da suka kashe ne saboda yana da hannu wurin kashe daya daga cikin shugaban su a jami'ar Ibadan a farkon wannan shekarar.

"An kuma gano cewa wadanda ake zargin sun saba kashe mutane musamman yan kungiyar da suke adawa da su a Ikorodu da kewaye. Saheed Gbadebo shi kadai ya kashe mutum biyu a Bayekun Street, Ikorodu, da mutum biyar a Ajah.

"Za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel