Wata sabuwa: Ana bincikar Magu a kan mallakar kadarori a Dubai
Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, na sake fuskantar kalubale da zargi. Ana zarginsa da mallakar kadarori a Dubai.
Dakataccen shugaban EFCC, wanda ke hannun 'yan sanda tun daga ranar Litinin, an ci gaba da tuhumarsa a ranar Laraba.
Jaridar The Punch ta gano cewa, wani sabon zargi ya bullo bayan zaman ranar Laraba, lamarin da yasa aka sake tsaresa.
Jami'an tsaron farin kaya ne suka tsare Magu a gaban tsohuwar hedkwatar EFCC da ke titin Fomella, Wuse 2 a Abuja, a ranar Litinin kuma suka tasa keyarsa zuwa fadar shugaban kasa.
Yana ofishin 'yan sanda da ke Garki tun daga ranar Litinin inda daga nan aka mika shi fadar shugaban kasa don ci gaba da bincikarsa.
Kamar dai yadda al'amarin ranar Litinin da Talata ya faru, an ci gaba da tuhumar Magu amma an hana manema labarai shiga wurin ko a ranar Laraba.
Wasu daga cikin manema labarai na gidan gwamnatin da suka yi yunkurin shiga wurin an dakatar dasu.
Hatta wadanda suka yi yunkurin ajiye ababen hawansu a gaban wurin, an bukacesu da su yi amfani da sauran wuraren ajiye ababen hawa da ke fadar shugaban kasar.
The Punch ta gano cewa, kwamitin da ke tuhumar Magu karkashin shugabancin Mai shari'a Ayo Salami, na kokarin gano cewa Magu ya siya kadarori a Dubai, inda ya dinga ziyara ba tare da sanin gwamnati ba.
KU KARANTA: Alkali ya daure ma'auratan da suka kafa wa 'yar aiki kusa a kai, konata da kuma saka mata makami a gaba
Wata majiya ta ce, kwamitin binciken zai duba duk takardun da aka samu a gidan Magu tare da yin kiyasi a kan albashinsa da kuma kudin da ke shiga asusun bankinsa.
Majiyar ta ce, "kwamitin na kokarin tantance zargin da ake wa Magu na cewa ya mallaki wasu kadarori a Dubai da sauran sassan duniya. Ana bincikar kuma yadda ake waskar da kudin da aka kwato bayan an hadame.
"Ban san nisan da kwamitin yayi wurin bincike ba. Amma suna kokarin bincike a kan takardun da aka samo daga gidansa da kuma ofishinsa don yin kiyasi."
Bayan kammala tuhumarsa na sa'o'i 8 a ranar Laraba, an mayar da Magu wurin 'yan sanda inda ya kwana a ranakun Litinin da Talata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng