Dawowar jigilar mutane: Sharuda 10 da FAAN ta gindayawa Fasinjoji da kamfanonin jirage

Dawowar jigilar mutane: Sharuda 10 da FAAN ta gindayawa Fasinjoji da kamfanonin jirage

A yau, Laraba, ne kamfanonin jiragen sama suka dawo jigilar mutane a cikin gida Najeriya bayan janye dokar hana zirga - zirga a tsakanin jihohi sakamakon bullar annobar korona.

Hukumar da ke alhakin kula da filayen jiragen sama da harkokin da suka fasinjoji (FAAN) ta fitar da jerin wasu matakai da ake bukatar Fasinjoji da kamfanonin jirage su kiyaye da su domin kaucewar yaduwar cutar korona.

Ga jerin matakan guda 8;

1. Saka takunkumin fuska ya zama wajibi ga dukkan fasinjoji kafin su shiga jirgi

2. Dole Fasinjoji su wanke hannayensu da sinadarin tsaftace hannu na musamman da kuma sinadarin da ke kashe kananan kwayoyin cuta.

3. An bukaci Fasinjoji su bawa juna tazarar taku 6 yayin da suke kan layin shiga jirgi

4. Ana son fasinjoji su kasance a filin jirgi sa'o'i uku kafin tashin jirgi

5. Ba za a bar 'yan rakiya su shiga wurin da ake tantance matafiya kafin su tashi ba

6. An shawarci ma su zuwa daukan fasinjoji su kasance a cikin motocinsu har sai matafiya sun fito harabar ajiye motoci bayan sauka daga jirgi

7. An gargadi matafiya da sauran jama'a su guji taba abubuwa a filin jirgi ba tare da wani dalili ba

8. Za zana layuka domin nunawa matafiya wurin da ya kamata su tsaya yayin da suke kan layin tantancewa a filin jirgi

9. Za a ke gwada yanayin dumin jikin fasinjoji a filayen jirgi

10. Kamfanonin jirage su samar da ma'aikatan da za su ke digawa Fasinjoji sinadarin kashe kwayoyin cuta a hannu a bakin kofar shiga jirgi.

Dawowar jigilar mutane: Sharuda 10 da FAAN ta gindayawa Fasinjoji da kamfanonin jirage
Hadi Sirika; ministan sufurin jiragen
Asali: Twitter

A ranar Talata ne kasar Dubai ta sanar da bude iyakokinta ga bakin haure ma su yawon bude ido bayan shafe kusan watanni hudu a karkashi dokar kulle.

Gwamnatin kasar ta ce za a gudanar da gwajin cutar korona a kan dukkan bakon da ya shiga kasar.

DUBA WANNAN: An gano gawar mutane 180 a wani kabari a kauyen Djibo

Bude iyakokin kasar ga ma su yawon bude ido na zuwa ne a daidai lokacin da adadin wadanda suka kamu da cutar korona ya hau sama zuwa mutum 52,068 da suka hada da mutane 324 da suka mutu.

Yawancin bakin haure 'yan ci rani na zaune ne a cakude cikin takura a muhallinsu lamarin da ya haifar da yawaitar ma su cutar korona a cikinsu.

Ana bukatar bakin da za su shiga kasar su gabatar da takardar shaidar yi mu su gwajin cutar korona a cikin kwanaki hudu kafin barin kasarsu.

Gwamnatin kasar ta ce za ta gudanar da gwajin korona nan take a kan duk wani bako da bashi da takardar shaidar yi ma sa gwajin korona daga kasarsa, sannan tilas ya killace kansa har sai sakamakon gwajinsa ya fito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel