Gwamna Wike ya sallami babban sakatare saboda saba dokar korona

Gwamna Wike ya sallami babban sakatare saboda saba dokar korona

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya kori sakataren dindindin, Sunny Okere, saboda karya dokokin kiyaye yaduwar annobar coronavirus da aka saka a jihar.

Hakan na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Paulinus Nsirim ya fitar a ranar Laraba kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar sanarwar, korar da aka yi wa Okere za ta fara aiki nan take.

Wike ya tuɓe babban sakatare saboda saba dokar korona
Nyesome Wike. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Covid-19: Wani mutum ya siya takunkumin fuska ta gwal kan kudi N1.5m (Hotuna)

An kori tsohon sakataren na dindindin ne saboda ya hallarci wata jana'iza inda fiye da mutum 50 suka hallara wadda hakan ya saba dokar jihar ta gudanar da jana'iza yayin annobar Covid-19.

An ruwaito cewa gwamnan ya ce, "A yayin da ake kara samun yaduwar cutar da hatsari ga lafiyar mutane, mafi yawancin mutanen gari ba su bin dokokin da aka shimfida don kare lafiyarsu.

"Masu motocin kansu da motoccin haya, masu kamfanoni da yan kasuwa da coci-coci duk ba su kiyaye sharrudan da aka gindaya domin dakile yaduwar cutar.

"Ana yin janaiza ba tare da bin sharrudan da aka gindaya ba na cewa kada mutane su wuce 50 a wurin jana'izan abin mamaki har wani sakataren dindindin ne ya kori jami'an Ma'aikatan Lafiya ta Jiha da suka tafi wurin domin tabbatar da an bi doka a Oyigbo.

"Saboda haka, an sallami sakataren dindindin, mai kula da bin tsare tsare, Mr Sunny daga aikinsa nan take saboda saba dokar jana'iza yayin annobar corona.

"Wannan zai zama darasi ga dukkan sauran ma'aikatan gwamnati da ke da niyyar saba dokoki."

Gwamnan ya bawa maaikatan lafiya a jihar tabbacin cewa jihar za ta cigaba da kulawa da walwalarsu a yayin da suke cigaba da yi wa jihar hidima duk da hatsarin da rayuwarsu ke ciki.

Ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin daukan duk wata mataki da za ta dakile yaduwar cutar a cikin mutane.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi feshin magunguna a makarantu ta yadda za su kasance a shirye a duk lokacin da aka tabbatar daliban ba su cikin hatsarin kamuwa da cutar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel