Tsofaffin gwamnoni 4 da Magu ya sa aka tura gidan yari

Tsofaffin gwamnoni 4 da Magu ya sa aka tura gidan yari

A wani yanayi da 'yan Hausa na iya kiransa da reshe ya juye da mujiya, a halin yanzu farautar da shugaban hukumar EFCC mai yaki da rashawa Ibrahim Magu ya saba yi, ta juya kansa.

Tun a ranar Litinin ne Magu ya bayyana a gaban kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na karkatar da akalar wasu kudade ta hanyar da ba su dace ba.

Kwamitin wanda Tsohon alkalin kotun daukaka kara, Mai Shari'a Ayo Salami yake jagoranta, ya gayyaci Magu domin ya wanke kansa daga laifukan da ake zargin ya aikata yayin jagoranci a hukumar ta EFCC.

Gabanin yanzu, Magu shi ne jagoran hukumar EFCC mai farauto mutanen da ake zargi da aikata wani laifi da ya danganci yi wa tattalin arzikin kasar nan ta'annati.

Tun a shekarar 2015 ne shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jagoran hukumar EFCC, sai dai har kawo yanzu, majalisar dattawan kasar ba ta amince da nadinsa ba kamar yadda doka ta tanada.

A fafutikar da ya rika yi ta sauke nauyin da rataya wuyansa, ya cafke da dama daga cikin manyan 'yan siyasar kasar tare da gurfanar da su a gaban kuliya, inda har a wasu lokutan ma ya kan yi nasarar tasa keyarsu har gidan kaso.

A wani rahoto da muka kalato daga sashen Hausa na BBC, an ruwaito jerin wasu bajiman 'yan siyasa da Magu ya samu nasarar turawa gidan cin sarka bayan kotu ta tabbatar da laifikan da ake tuhumarsu da su.

Ga jerin tsofaffin gwamnonin kamar haka:

1. James Bala Ngilari

James Bala Ngilari
Hoto daga; Ripplesnigeria.com
James Bala Ngilari Hoto daga; Ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Ngilari shi ne tsohon gwamnan jihar Adamawa, wanda aka jefa gidan yari a 2017 kuma zai kwashe shekaru 5 kan laifin almundahanar Naira miliyan 167.

Wata kotu a Yola ta samu gwamnan da laifi tare da daure shi tsawon shekara biyar, amma daga baya kotun daukaka kara ta jihar ta sauya hukuncin, inda ta ce tuhume-tuhuen da ake masa ba su da hujja.

2. Jolly Nyame

Jolly Nyame
Hoto daga; Premium Times
Jolly Nyame Hoto daga; Premium Times
Asali: Depositphotos

Nyame wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Taraba, ya shiga gidan yari tun a shekarar 2018 kuma zai kwashe shekaru 14 kan laifin karkatar da kudin baitul mali lokacin da yake gwamnan jihar a tsakanin shekarar 199 zuwa 2007.

3. Joshua Dariye

Joshua Dariye
Hoto daga; Premium Times
Joshua Dariye Hoto daga; Premium Times
Asali: Depositphotos

Dariye wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Filato, ya shiga gidan yari tun a shekarar 2018 kuma zai kwashe shekaru 14 kan laifin facaka da naira biliyan 1.162.

Daga bisani kotun kolu ta yi masa sassauci idan ta rage yawan shekarun zuwa 10.

KARANTA KUMA: Doka ta 10: Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun gana a ranar Laraba

4. Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu
Asali: UGC

An yankewa tsohon gwamnan jihar Abiya hukuncin daurin shekaru 12 kan laifin almundahanar Naira biliyan 7.65 a yayin da yake gwamna tsakanin shekarar 1999 da 2007.

A yanzu haka Sanata ne kuma daya daga cikin shugabannin majalisa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel