Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG

Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG

Ɗaliban Najeriya da ke ajin karshe a makarantun sakandare ta gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC ba a bana a cewar gwamnatin tarayya.

Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Laraba bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC.

Ya kuma kara da cewa har yanzu ba a tsayar da ranar da za a bude makarantun ba a kasar kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Adamu ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da ke shirin bude makarantu su hakura su canja shawara saboda annobar korona.

"Ina kira ga gwamnatocin jihohi da suka amince za su bude makarantu su sake shawara saboda halin da muke ciki na annobar COVID-19. Ina ganin akwai hatsari cikin yin hakan. Mu kare yaran mu," in ji shi.

Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG
Daliban Najeriya ba za su rubuta WAEC ba a 2020 – FG
Asali: UGC

Ya ce dukkan makarantun da ke karkashin gwamnatin tarayya za su cigaba da kasancewa a rufe har sai an tabbatar an ci galaba a kan cutar korona.

Ministan ya yi kira ga hukumar shirya jarrabawar ta Afirka ta Yamma, WAEC, da gwamnatocin jihohi su canja shawarar su ta bude makarantu don yin jarrabawa.

A cewar Adamu, Hukumar WAEC ba ta da ikon fada wa makarantu lokacin da za su bude.

DUBA WANNAN: Covid-19: Wani mutum ya siya takunkumin fuska ta gwal kan kudi N1.5m (Hotuna)

Ya ce ya gwammace daliban Najeriya su rasa shekarar karatu daya a maimakon jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Har wa yau, Ministan ya bayyana cewa za a yi wa dakunan kwanan daliban Kwallejin Fasaha ta Kaduna, Kadpoly, gyara.

Ya ce wani mai saka hannun jari ne ya bayar da kudi N774,264,000 don yin gyaran.

Ya tabbatar wa daliban kwallejin cewa gyaran ba zai saka ayi musu karin kudin dakunan kwanan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel