An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

An haifi wani jinjiri rike da na'urar hana daukan ciki da ya dace ya hana mahaifiyarsa daukan juna biyun da ta haife shi.

An haifi jinjirin ne a asibitin Hai Phong International da ke birnin Hai Phong a arewacin kasar Vietman kamar yadda LIB ta ruwaito.

Hotunan jinjirin da aka dauka ya nuna shi yana rike da na'urar hana daukan cikin mai launin baki da ruwan dorawa a hannunsa.

An haifi jariri rike da naurar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)
An haifi jariri rike da naurar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)
Asali: UGC

Kamata ya yi na'urar ta hana maniyin mahaifinsa haduwa da kwayayen haihuwar mahaifiyarsa.

Likitan mata, Tran Viet Phuong ta ce naurar ta fito ne bayan da aka haifi jinjirin. Jinjirin ya rike na'urar a hannunsa yayin da aka dauki hoton kamar yadda aka yi ikirari.

Dr Phuong ta shaidawa kafafen watsa labarai na kasar cewa, "Bayan an haife shi, na yi tunanin abin sha'awa ne yadda ya rike na'urar a hannunsa, sai na dauki hotuna. Ban yi tsammanin hotunan za su dauki hankalin mutane ba."

An haifi jariri rike da naurar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)
An haifi jariri rike da naurar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna). |Hoto daga LIB
Asali: UGC

Mahaifiyar jinjirin mai shekaru 34 ta yi ikirarin cewa an saka mata na'urar ne tun shekaru biyu da suka gabata amma bai yi aiki ba domin daga bisani ta gano cewa ta dauki juna biyu.

DUBA WANNAN: Covid-19: Wani mutum ya siya takunkumin fuska ta gwal kan kudi N1.5m (Hotuna)

Dr Phuong ta ce akwai yiwuwar na'urar ta matsa daga ainihin wurin da aka saka shi ne hakan yasa bai yi aikin da ya dace ya yi ba na hana daukan ciki shi yasa mahaifiyar ta samu juna biyu.

An haifi jariri rike da naurar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)
An haifi jariri rike da naurar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna). Hoto daga LIB
Asali: UGC

Rahotanni sun ce jinjirin lafiyarsa kalau lokacin da aka haife shi. Nauyinsa ya kai kilogram 3.17 kuma har yanzu jinjirin da mahaifiyarsa suna asibiti ana kulawa da su.

Mahaifiyar jinjirin tana da wasu yara biyu a cewar rahotanni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel