An yi mummunar gobara a wata cibiyar hako man fetur ta kamfanin NNPC

An yi mummunar gobara a wata cibiyar hako man fetur ta kamfanin NNPC

Ana tsaka da gudanar da aiki, kwatsam wuta ta kama a daya daga cikin cibiyoyin hako mai na kamfanin man fetur na kasa, NNPC, lamarin da ya janyo mutuwar ma'aikata bakwai nan take.

Kamfanin NNPC a ranar Laraba ya sanar da cewa, wata wuta da ta tashi a daya daga cibiyoyinta na hako man fetur da ke gabar Kogin Benin, ta yi sanadiyar salwantar rayukan ma'aikata bakwai.

Babban jami'in sadarwa da kula da sashen hulda da al'umma na kamfanin, Kenni Obateru, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Obateru ya ce wannan ibtila'i ya auku ne a ranar Talata.

An yi mummunar gobara a wata cibiyar hako man fetur ta kamfanin NNPC
Hakkin mallakar Hoto; Jaridar Daily Nigerian
An yi mummunar gobara a wata cibiyar hako man fetur ta kamfanin NNPC Hakkin mallakar Hoto; Jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ya ce "wannan mummunan tsautsayi ya auku ne a ranar Talata yayin dasa wani tsani a gabar Kogin Benin wanda zai samar da wani dandamali a matsayin hanyar shige da fice yayin hako mai."

"Abin takaici ne mun yi asarar rayukan ma'aikata bakwai."

Kamfanin ya sanar da cewa an fara gudanar da binciken diddigi domin gano musabbabin da ya haddasa tashin wutar.

Mai magana da yawun kamfanin, ya ce tuni an sanar da hukumar da ke kula da albarkatun man fetur ta kasa DPR, kamar yadda dokokin aiki suka tanada a irin wannan yanayi.

KARANTA KUMA: Rundunar Sojin kasa ta ragargaji mayakan Boko Haram a Damboa

Ya bayyana cewa, an killace gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a ɗakin ajiye gawawwaki na Sapele, yayin da kuma aka tuntubi iyalansu.

Manajan Darakta na kamfanin, Mele Kolo Kyari, ya jajantawa iyalan ma'aikatan da mai yankan kauna ta katsewa hanzari.

Ya roki Mai Duka ya ba su ikon hakuri da juriyar wannan mummunan rashi da suka yi na makusantansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel