Ta'addanci: An kama mata da miji da manyan bindigu a jihar Kebbi

Ta'addanci: An kama mata da miji da manyan bindigu a jihar Kebbi

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kebbi, ta cafke wani mutum da ake zargi dan daban daji ne dauke da man bindigu biyu kirar AK-47 a kwaryar Birnin Kebbi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, Agunbiade Oluyemi-Lasore, shi ne ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai cikin babban birnin jihar a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa, an cafke mutumin da ake zargi tare da matar sa a ranar 29 ga watan Yuni, yayin da wata tawagar 'yan sanda ke gudanar da bincike a kan hanyar garin Birnin Yauri zuwa Zuru.

Sufeto Janar na 'yan sanda; IGP Muhammad Adamu
Hakkin mallakar hoto; Premium Times
Sufeto Janar na 'yan sanda; IGP Muhammad Adamu Hakkin mallakar hoto; Premium Times
Asali: Twitter

“A ranar 29 ga Yuni, wata tawaga 'yan sanda yayin da suke bakin aiki a kan titin Birnin Yauri zuwa Zuru, sun kama Umaru Usman, wani mutumin kauyen Zangon Labandi na karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

"An kuma kama shi tare da matarsa, Halima Adamu, dauke da manyan bindigogi biyu kirar AK 47 da kuma alburushai 154."

"Haka zalika jami'an 'yan sandan sun kamu ma'auratan da kakin sojoji da kuma layu a tattare da su."

A yayin gudanar bincike, an kuma kama Taru Mai Unguwa, wani mutumin kauyen Danmaraya na karamar hukumar Ngaski ta jihar Kebbi, da ya ke tattaro wa 'yan ta'adda bayanan sirri.

KARANTA KUMA: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

Kwamishinan 'yan sandan ya ce za a gurfanar da ababen zargin biyu a gaban kuliya da laifin mallakar makamai da kuma dayan mai laifin cin amanar kasa.

Mista Oluyemi ya kara da cewa, rundunar 'yan sandan ta kuma samu nasarar kama wasu mutum 16 da ake zarginsu da ta'addanci kama daga garkuwa da mutane, fashi da makami da sace-sace da suka addabi al'ummar jihar.

A wani rahoto da Legit.ng ta ruwaito, rundunar 'yan sanda ta kama wani da ake zargin dan fashi ne mai shekara 30, Abubakar Namalika.

Namalika ya amsa laifin cewa yana daga cikin wadanda suka kashe wani likita.

Likitan da suka kashe mai suna Okpara Enoch, ya kasance ma'aikaci a cibiyar kiwon lafiya ta tarraya da ke Gusau, jihar Zamfara.

Ya ce ya samu tukwicin N5,000 kan kashe mutane bakwai da ya yi ciki harda marigayi Dr. Opara, jaridar The Nation ta ruwaito.

Mai laifin ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan kwamishinan yan sandan jihar Zamfara ya gurfanar da shi a hedkwatar rundunar da ke Gusau a ranar Litinin.

A cewarsa, wani Shehu Bagewaye, shugaban kungiyarsu yana aiken su sato bayin Allah amma sai ya basu kaso kadan bayan ya karbi kudin fansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel