Yanzu-yanzu: Rikicin siyasar APC ya dau sabon salo a Ondo, an dakatad da mataimakin kakakin majalisa

Yanzu-yanzu: Rikicin siyasar APC ya dau sabon salo a Ondo, an dakatad da mataimakin kakakin majalisa

Rikicin siyasar jam'iyyar All Progressives Congress APC da tayi tasiri ka majalisar dokokin jihar Ondo ta dau sabon salo a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, 2020.

A yau, shugabannin majalisar sun dakatad da mataimakin kakakin majalisar, Hanarabul Irouju Ogundeji, tare da wani mamban majalisar, Adewale Willams.

Yan majalisan biyu na cikin mambobin majalisar guda tara (9) da suka janye hannunsu daga shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi.

An dakatad da su ne bisa laifin rashin da'a.

A jiya Talata, 'Yan majalisar jihar Ondo tara sun tsame kansu daga kokarin tsige mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi.

Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, 'yan majalisar jihar Ondo sun fara shirin tsige mataimakin gwmanan jihar, Mr Agboola Ajayi.

Yan majalisar sun tattaunawa a zauren majalisar a kan zargin saba dokokin aiki da ake yi wa mataimakin gwamnan.

Bayan tattaunawar, Majalisar ta cimma matsayar aike wa mataimakin gwamnan takardar sanar da tsige shi.

Jami'an 'yan sanda da na hukumar tsaro ta NSCDC sun mamaye harabar majalisar domin tabbatar da doka da oda.

Yanzu-yanzu: Rikicin siyasar APC ya dau sabon salo a Ondo, an dakatad da mataimakin kakakin majalisa
Yanzu-yanzu: Rikicin siyasar APC ya dau sabon salo a Ondo, an dakatad da mataimakin kakakin majalisa
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, a ranar Talata, 2 ga watan Yuli, gwamnan jihar Ondo, ya sanar da cewa ya kamu da cutar COVID-19.

Amma Akeredolu ya bayyana cewa duk da cewa yana killace, ba zai mika ragamar mulki hannun mataimakinsa ba.

Gwamnan ya shiga takun tsaka da mataimakinsa tun gabanin zaben Shugaban kasa a 2019.

Haka suka cigaba da zaman doya da manja har sai yanzu da mataimakin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP.

A lokacin da cutar Korona ta kama Gwamnan, mataimakin ya bukacesa ya mika masa ragamar mulki tunda yana kwance yanzu.

Gwamnan yace sam ba zai mika masa ba.

Daga baya mataimakin ya baiwa gwamnan wa’adin kwanaki 21 ya mika masa mulki ko su garzaya kotu.

Amma cikin kwanaki bakwai, Gwamnan ya samu lafiya.

Daga samun lafiyarsa kuma, Mista Idefayo Abegunde, sakataren gwamnatin jihar Ondo, ya yi murabus daga mukaminsa a yau, Litinin, 06 ga watan Yuli, 2020.

Abegunde ya bayyana cewa dalilin da yasa yayi murabus shine gwamnan ya gaza kuma a hakikanin gaskiya bashi ya lashe zabe a 2016 ba.

Shi kuma Gwamnan ba tare da bata lokaci ba ya maye gurbinsa da Taiwo Oluwatuyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel