Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa
- Buhari ya jagoranci zaman majalisar zantarwa karo na shida ana kiyaye dokar nesa-nesa da juna
- Ministoci 11 sun halarci zaman majalisar da shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba, 8 ga watan Yuli
- Yayin zaman majalisar, an yi alhinin mutuwar tsohon ministan wasanni da matasa, Alhaji Inuwa Abdulqadir
A yau Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar gwamnatinsa ta Aso Villa da ke babban birnin Tarayya Abuja.
Wannan shi zaman majalisar na shida da shugaban kasar ya jagoranta da aka kiyaye dokar nesa-nesa da juna inda ta hanyar amfani da yanar gizo wajen tattaunawa.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ministocin da a dole su na da ta cewa kuma su na dauke da bayanan da za su gabatar su ne kadai suka halarci zaman majalisar a fadar shugaban kasa.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Kusoshin gwamnatin da suka halarci zaman a wannan mako sun hadar da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.
Ministoci 11 ne suka halarci zaman ciki har da;
Ministan kasafi da tsare-tsaren - Zainab Ahmed
Ministan Sufuri - Honarabul Rotimi Amaechi
Ministan Labarai da Al'adu - Alhaji Lai Mohammed
Ministan Ayyuka da Gidaje - Mista Babatunde Fashola
Ministan Sufurin Jiragen Sama - Sanata Hadi Sirika
Ministan Shari'a Kuma Lauyan Koli na Kasa - Abubakar Malami
Ministan Harkokin Neja Delta - Godswill Akpabio
Ministan Harkokin Waje - Geoffery Onyeama
Ministan Ayyuka na Musamman - George Akume
Ministan Ilimi - Adamu Adamu
Karamin Ministan Harkokin Waje - Ambasada Zubairu Dada.
KARANTA KUMA: WAEC ta shata sharudan zana jarrabawar bana
Gabanin fara tattaunawa kan al'amuran da suka shafi zaman majalisar na yau, shugaba Buhari ya nemi da a yi shiru na minti daya domin yin alhinin mutuwar tsohon ministan wasanni da matasa; Inuwa Abdulqadir.
Marigayi Inuwa yan daya daga cikin mambobin tsohon kwamitin gudanarwa kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa reshen Arewa mao Yamma, wanda ajali ya katse masa hanzari a ranar Litinin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng