WAEC ta shata sharudan zana jarrabawar bana

WAEC ta shata sharudan zana jarrabawar bana

Hukumar WAEC mai shirya jarrabawa kammala karatun sakandire a Yammacin Afrika, a ranar Talata ta fitar da ka'idodin yadda za'a gudanar da jarrabawar a bana.

Shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Mista Patrick Areghan, ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki da su tanadi kudaden samar da kayan kariya ga ma'aikatan da za su gudanar da jarrabawar.

Ya ce hukumar ta shimfida matakai da ka'idodin da dole sai an kiyaye yayin gudanar da jarrabawa a makarantu daban-daban da ke yankin Afrika ta Yamma.

Shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Mista Patrick Areghan
Hakkin mallakar hoto; WAEC
Shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Mista Patrick Areghan Hakkin mallakar hoto; WAEC
Asali: Twitter

Mista Patrick ya ce a yayin shimfidar matakan da ka'idodi, hukumar ta yi la'akari da hanyoyi da kuma sharudan da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka gindaya da manufar dakile yaduwar cutar korona.

Daga cikin sharudan da hukumar ta shata sun hadar da:

1. Tanadar wuraren wanke hannu da sabulu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin tsaftace hannu (sanitizer).

2. Wajibi ne kowace makaranta ta mallaki nau'rar daukan dumin jiki domin tantance marasa lafiya.

3. Dukkanin masu ruwa da tsaki yayin jarrabawar sai sun saka takunkumin rufe fuska tare da wanke hannaye a kai-a kai a kullum har zuwa lokacin da za a kammala jarrabawar.

4. Kiyaye dokar nesa-nesa da juna ya zama tilas. Za a sanya mazaunin kowace dalibi tare da bayar da tazara ta tsawon mita biyu a tsakani.

Hakan yana nufin sai an tanadi karin mutanen da za su rika duba dalibai da kuma ajujuwan da dalibai za su yi zaman zana jarrabawar.

Sai dai ya ce ko shakka babu, wannan lamari yana bukatar kudi, musamman wajen tanadar kayayykin kare kai ga jami'an hukumar da za su jibinci lamarin gudanar da jarrabawar.

KARANTA KUMA: Buhari ya fara laluben wanda zai maye gurbin Magu

Legit.ng ta ruwaito cewa, Hukumar WAEC, a ranar Talatar da ta gabata ta sanar da fidda jadawalin jarrabawar shekarar 2020.

Babban jami'in hukumar WAEC a Najeriya, Mista Areghan, shi ne ya bayyana a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin kasar na tarayya wato Abuja.

Ya tunatar da manema labarai yadda annobar korona ta wajabta dage jarrabawa wadda a baya aka kudiri gudanar da ita a tsakanin ranar 6 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Yuni.

Ya ce a halin yanzu bayan bita kan halin da ake ciki, za a gudanar da jarrabawar cikin tsawon lokacin da bai wuce makonni biyar ba, daga ranar 3 ga watan Agusta zuwa 4 ga watan Satumba.

Mista Patrick ya ce za rika gudanar da jarrabawar tun daga ranar Litinin har zuwa Asabar domin samun damar kammala ta cikin makonni biyar.

Ya ce dalibai 1,549,463 ne suka yi rajistar zana jarrabawar a bana daga makarantu 19,129, inda 786,421 suka kasance maza yayin da kuma 763,042 suka kasance mata.

Ya gargadi dukkanin makarantu da dalibai da su guji duk wasu ababe na satar jarrabawa tare da cewa rashin aiwatar da kyakkyawan shiri ba zai taba zama uzuri na saba wa doka ba.

A karshe ya sanar da cewa, an aike da jadawalin karshe na jarrabawar bana ga ofisoshin hukumar na yankuna da rassa daban-daban da kuma ma'aikatun ilimi na gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel