Bayan bincike gidansa, an cigaba da tsare Magu a ofishin yan sanda

Bayan bincike gidansa, an cigaba da tsare Magu a ofishin yan sanda

- Tuhume-tuhumen da ake yiwa shugaban EFCC na da matukar girma - Babban Jami'i

- Kungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta yi amanna da binciken, Magu bai fi karfin doka ba

Bayan wasu jami'an 'yan sanda da ke aiki da sashen binciken manyan laifuka (FCIID) sun birkice gidan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaba Buhari ya dakatar, ya yi kwanansa na biyu a tsare.

A ranar Talata, wasu jami'an FCID sun kai simame gidan Magu dake titin Abduljalil a unguwar Karu da ke wajen birnin tarayya, Abuja.

Hakazalika ranar Talata, kwamitin binciken Magu karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara, Ayo Isa Salami, ta cigaba da yi masa tambayoyi.

Bayan kammala zaman jiya misalin karfe 8:30na dare, an sake mayar da shi ofishin yan sanda inda ya kwana.

Wata majiya ta bayyanawa The Punch cewa "Lallai an mayar da Magu wajen yan sanda. Ya bar inda kwamitin ke bincike misalin karfe 8:30 na dare kuma aka mayar da shi ofishin yan sandan da aka tsareshi ranar Litinin."

.KU KARANTA: Jerin tuhume-tuhume 10 da ake yiwa shugaban EFCC, Ibrahim Magu

Bayan bincike gidansa, an cigaba da tsare Magu a ofishin yan sanda
Bayan bincike gidansa, an cigaba da tsare Magu a ofishin yan sanda
Asali: UGC

A ranar Litinin, wasu jami'an tsaro sanye da kayan gida sun tare shugaban EFCC, Ibrahim, Magu daga shiga ofishinsa kuma suka bayyana masa cewa ana bukatarshi a fadar shugaban kasa.

Zuwansa ke da wuya ya fuskanci kwamiti na musamman domin yi masa tambayoyi bisa wasu tuhume-tuhume 22 da ministan shari'a, Abubakar Malami, ke masa.

Ba tare da bata lokaci ba aka kaddamar da bincikekan lamarin har zuwa misalin karfe 10:15 na dare, sannan jami'an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa kuma ya kwana a hannunsu.

A ranar Talata, Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC zuwa lokacin da za'a kammala bincike.

Buhari ya nada Magu ne a watan Nuwamba, 2015, watanni biyar bayan hawa mulki.

Yayinda ya gabatar da sunansa Majalisar dattawa domin tabbatar da shi, yan majalisar suka ki saboda rahoton DSS dake zarginsa da wasu laifukan rashawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel