Jami'an Kwastam da DSS sun kai simame Kasuwar Singer dake Kano, sun kwace kayayyaki

Jami'an Kwastam da DSS sun kai simame Kasuwar Singer dake Kano, sun kwace kayayyaki

Hukumar hana fasa kwabrin tare da hadin kan hukumar leken asirin cikin gida DSS sun kai simame kasuwar Singer dake jihar Kano don dakile masu shigo da haramtattun kaya Najeriya.

Yayin farmakin, jami'an sun damke mutane uku yayinda aka kwace dukiyoyin kimanin N1.4million a kasuwar.

A hirar da Daily Trust tayi da Kwantrolan hukumar kwastam, shiyar Kano/Jigawa, Nasir Ahmed, ya ce manufar kai harin shine ya zama izina ga wadanda ke shigo da haramtattun kaya da masu sayarwa.

Ya ce dukkansu su sani cewa hukumar Kwastam na kallonsu kuma ba zasuyi kasa a gwiwa wajen hana fasa kwabrin kayayyaki ba.

Daga cikin kayayyakin da aka kwace akwai Shinkafa, galolin mai, kwalayen taliya da sauran su.

Jami'an Kwastam da DSS sun kai simame Kasuwar Singer dake Kano, sun kwace kayayyaki
Wasu daga cikin kayan da aka kwace
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dalolinka ba za suyi aiki a Edo ba - Gwamna Wike ga Ganduje

Yace: "Muna son sanar da mutane cewa ba zasu saba doka kuma su tsira ba. Mun yi yarjejeniya da shugabannin kasuwar Singer kuma suna kokarin cikawa, amma wasu kananan yan kasuwa na kokarin karya alkawari ta hanyar sayar da haramtattun kaya."

Ya ce abinda wadannan yan kasuwan ke yi na cutar da tattalin arzikin kasa, kuma hukumar za tayi iyakan kokarinta wajen kare muradan Najeriya.

Yayinda aka tambayeshi shin ta yaya masu fasa kwabri ke samun nasarar shigo da kaya ta iyakokin Najeriya, Nasir ahmed ya ce jami'an kwastam na iyakan kokarinsu amma wasu mazauna iyakokin Najeriya ke taimakawa yan fasa kwabri.

Yace: "Kwanan nan, yan fasa kwabri sun kaiwa jami'anmu hari kuma mutanen yankin Nijar sun taimakawa yan sumogulan har da tayasu shigarda motarmu kasar Nijar kuma suka lalata.

"Saboda haka kun ga yadda makwabtanmu ke cin zarafinmu saboda an haramta shigo da shinkafa."

Mutane ukun da aka kama sune Akibu Alasan, Auwalu Shehu da Yahuza Muhammad Sani kuma za'a gurfanar da su a kotu bayan bincike, Ahmed ya laburta

Amma a cewar wadanda aka kama, sun ce ba kayayyakinsu bane, wani direba ne ya basu ajiya.

Jami'an Kwastam da DSS sun kai simame Kasuwar Singer dake Kano, sun kwace kayayyaki
Wadanda aka kama
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng