Dakarun Soji sun ragargaji yan bindiga a Batsari, sun hallaka 46

Dakarun Soji sun ragargaji yan bindiga a Batsari, sun hallaka 46

Dakarun Sojin musamman na Super Camp 4 Faskari, dake aiki karkashin atisayen 'tsarkake Sahel' sun hallaka yan bindiga akalla 46 a artabun da sukayi a jihar Katsina.

Sojojin sun dakile yan bindigan ne yayinda sukayi kokarin kawo hari garin 'Yar Gamji, dake karamar hukumar Batsari ta jihar.

Jagoran al'amuran yada labaran hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, a jawabin da ya saki jiya Litinin ya ce artabun ya auku ne ranar 6 ga Yuli, bayan kiran da suka samu daga al'ummar garin.

Enenche ya ce Sojin sun ragargaji yan bindigan ne bayan shugaban Sojin kasa, Tukur Buratai, ya kaddamar da atisayen, yayin murnar ranar Sojin shekarar 2020.

A cewarsa, Sojin sun yi musayar wuta da yan barandan kuma sun samu nasarar hallaka 46 cikinsu yayinda saura suka arce da raunukan harsashi.

Eneche ya yace yanzu haka Soji sun maye garin kuma suna gudanar da sintiri.

Dakarun Soji sun ragargaji yan bindiga a Batsari, sun hallaka 46
Dakarun Soji sun ragargaji yan bindiga a Batsari, sun hallaka 46
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Jami'an Kwastam da DSS sun kai simame Kasuwar Singer dake Kano, sun kwace kayayyaki

A wani labarin daban, Dakarun sojin Sector 3 OPERATION LAFIYA DOLE sun samu gagarumin nasara kan wasu yan ta'addan Boko haram da sukayi yunkurin kai musu hari a da safiyar Talata.

Hukumar Sojin ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita inda ta nuna hotunan yan ta'addan da suka kashe da kuma makaman da suka kwace.

Jawabin yace: "Jaruman Sojin Sector 3 OP LAFIYA DOLE sun ragargaji wasu yan ta'addan Boko Haram da sukayi kokarin shiga Monguno misalin karfe 11 na safiyar 7 ga Yuli, 2020."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel