Yadda wata mata ta shaƙe ɗan ta ya mutu saboda yana latsa waya cikin dare

Yadda wata mata ta shaƙe ɗan ta ya mutu saboda yana latsa waya cikin dare

Wata mata mai suna Alexandra Dougokenski ta kashe dan ta mai shekaru 11 ta hanyar sheke masa wuya saboda ta gaji da halinsa na buga wasar game a wayansa ta salula cikin dare.

A cewar Daily Mail, Yan sanda a kasar Brazil sun gurfanar da ita a kan zargin kashe dan ta mai suna Rafael a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli bayan ta amsa cewa ta aikata laifin.

Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan Rafael ya rubuta wasu baitocin waka inda ya ke bayyana irin kaunar da soyayya da ya ke yi wa mahaifiyarsa.

Yadda mahaifiya ta shaƙe ɗan ta ya mutu saboda yana latsa waya cikin dare
Alexandra Dougokenski da Rafael. Hoto daga Kanydaily
Asali: UGC

A cikin rubutun da ya yi, Rafael ya yi wa mahaifiyarsa godiya saboda kula da shi da ta ke yi da dan uwansa inda ya ce murmushinta ya fi masa komi a rayuwarsa.

DUBA WANNAN: An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna)

Matar mai shekaru 33 da farko ta yi ikirarin cewa yaron ya yi yunkurin tserewa daga gida ne bayan ta masa fada a kan halinsa na wasa da wayar salula da tsakar dare.

Masu bincike da yan uwa da abokansa sun taimaka wurin nemansa a wani daji da ke kusa da gidansu a Planato, jihar Rio Grande do Sul.

Bayan da aka yi ta nema ba a gano inda yaron ya ke ba, mahaifiyar ta fashe da kuka ta bayyana cewa ita ce ta shake shi da igiyar shanya tufafi a lokacin da ya bata mata rai.

Wacce ake zargin ta yi ikirarin cewa ta gaji da boye sirrin a zuciyarta kawai gara ta fadi gaskiya domin ta samu natsuwa.

Kwanaki goma bayan bacewarsa, ta bayyana inda ta boye gawar yaron nata.

An gano gawar yaron a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2020 cikin wani babban kwali a garejin gidan makwabtanta mai nisan mita 5.4 daga gidan iyayensu.

Gawar da aka gano ta fara rubewa inda aka nannade da wani zanin gado da kuma leda da aka rufe kansa da shi.

Alexandra Dougokenski bazawara ce domin ta dade da rabuwa da mahaifin yayan ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel