Dalolinka ba za suyi aiki a Edo ba - Gwamna Wike ga Ganduje

Dalolinka ba za suyi aiki a Edo ba - Gwamna Wike ga Ganduje

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a jiya ya caccaki takwararsa na jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, kan jawaban da yayi bisa zaben gwamnan jihar Edo da zai gudana ranar 19 ga Satumba, 2020.

Wike ya ce Ganduje ya sani cewa ba zai iya amfani da Dalolinsa ba wajen jan hankalin al'ummar jihar Edo.

Ganduje ne shugaban kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC na jihar Edo yayinda Wike ya kasance na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A taron rantsar da kwamitin yakin neman zaben PDP ranar Talata a Abuja, Wike yace: "Ganduje, Dalolinka ba zasuyi aiki ba a Edo. Muna da gaskiya a jam'iyyarmu,"

Dalolinka ba za suyi aiki a Edo ba - Gwamna Wike ga Ganduje
Dalolinka ba za suyi aiki a Edo ba - Gwamna Wike ga Ganduje
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa: "Kada ku raina abinda Ganduje ya fada, mu fahimce shi. Abinda yake fadi shine sun kammala shirin amfani da jami'an tsaro wajen tabbatar da cewa mutan jihar Edo sun gaza kare kur'iunsu."

"Ba zasu bari su fito zabe ba kuma kafin ku ankara, zasu sanar da sakamako."

"Wannan zaben, wajibi ne muyi nasara sosai. Babu wanda zai yi mana barazana."

"Bari in fada muku abinda ya sa suka nada Ganduje shugaban yakin neman zabensu, sabida Dalolin da suka gani ne."

"Amma abinda bai fahimta ba shine mu yan Niger Delta ne, zamu ci Dalarsa kuma mu durkusar da shi."

KU KARANTA: Bayan bincike gidansa, an cigaba da tsare Magu a ofishin yan sanda

A bangare guda, Gwamna Nyesom Wike, ya mayarwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, martani.

A ranar Litinin, Ganduje ya lashi takobin cewa APC zata ci mutunci Godwin Obaseki a Edo ta hanyar killace Wike.

Shi kuma Wike a martaninsa, ya ce mutumin da aka kama yana cusa dala cikin malin-malin ya kamata a killace, Sahara Reporters ta ruwaito.

Yace: "Tsakani na da mutumin da aka gani yana cusa Dala cikin aljihu, wa ya cancanci a killace?"

Hukumar gudanar da zabe INEC tace za'a gudanar da zaben gwamnan Edo ranar 19 ga Satumba, 2020.

Fasto Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC zai kara da Gwamna Godwin Obaseki na PDP wanda ke kan mulki yanzu.

Dukkansu sun sauya sheka daga jam'iyyunsu don takarar zaben. Yayinda Osagie Ize-Iyamu ya koma APC daga PDP, Obaseki ya sheka PDP daga APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel