COVID-19 ta harbi Malama, Yara, da Mai gidanta a Makarantar Ghana

COVID-19 ta harbi Malama, Yara, da Mai gidanta a Makarantar Ghana

Wani malami tare da mai dakinsa, da yara shida a makarantar Accra Girls Senior High School (AGISS) sun kamu da kwayar cutar COVID-19 a kasar Ghana.

Hakan ya faru ne mako guda bayan an bude makarantun kasar Ghana domin ‘daliban ajin karshe su shiryawa jarrabawar shiga ajin sakandare da masu haramar shiga makarantun gaba da sakandare.

Darekta janar na ma’aikatar lafiya, Dr. Patrick Kuma Aboagye da kuma takwaransa na ma’aikatar ilmi, Farfesa Kwasi Opoku-Agyemang su ka tabbatar da wannan a wani jawabi.

Jaridar Ghanaweb ta rahoto wannan a ranar Talata, 7 ga watan Yuli, 2020.

Zuwa jiya ranar Litinin, wannan makaranta ta AGISS ta samu mutane masu cutar COVID-19 takwas.

KU KARANTA: Wike ya maidawa Ganduje martani game da kalaman killace shi

COVID-19 ta harbi Malama, Yara, da Mai gidanta a Makarantar Ghana
Shugaban Ghana Nana Akufo Addo
Asali: Facebook

Jawabin ya ce: “Ma’aikatar ilmi ta samu rahoton wadanda ake zargi sun kamu da COVID-19 a makarantun boko irinsu Accra Girls Senior High school.”

“An sanar da ma’aikatar ilmi game da halin da ake ciki.” Inji Dr. Patrick Kuma Aboagye da Kwasi Opoku-Agyemang.

“Zuwa ranar 6 ga watan Yuli, 2020, yara shida, wata malamar makaranta, da mai dakinta sun kamu da COVID-19 a makarantar Accra Girls Senior High School.”

“Makarantar ta tsaurara matakai domin tabbatar da cewa ana bin dokokin hana cinkoso da saraun matakan rigakafin COVID-19 da wayar da kan ma’aikata, yaran makaranta da iyaye game da annobar.”

Hukumar ta sanar da jama’a cewa za ta yi bakin kokari wajen ganin an kare rayukan jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel