Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)

Dakarun sojin Sector 3 OPERATION LAFIYA DOLE sun samu gagarumin nasara kan wasu yan ta'addan Boko haram da sukayi yunkurin kai musu hari a da safiyar yau Talata.

Hukumar Sojin ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita inda ta nuna hotunan yan ta'addan da suka kashe da kuma makaman da suka kwace.

Jawabin yace: "Jaruman Sojin Sector 3 OP LAFIYA DOLE sun ragargaji wasu yan ta'addan Boko Haram da sukayi kokarin shiga Monguno misalin karfe 11 na safiyar 7 ga Yuli, 2020."

Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)
Asali: Twitter

Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)
Yanzu-yanzu: Jaruman Sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a Monguno (Hotuna)
Asali: Twitter

A bangare guda, A ranar Litinin, misalin karfe 5:30 na yamma dakarun sojin 198 Special Forces Battalion sun gamu da iftila'in bama-baman da aka shuka cikin kasa yayin sintiri a Mainok, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Humangle ta ruwaito cewa Bam din ya tashi da Sojin inda yayi sanadiyar mutuwar Hafsan Soja daya, Abdullahi Alhassan, mai matsayin 2nd Laftanar yayinda wasu Soji biyu suka jikkata.

Dakarun Sojin fiye da 12 na cikin motocin yaki biyu ne lokacin da Bam din ya tashi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel