Labari da duminsa: 'Yan majalisa 9 sun janye kansu daga yunkurin tsige mataimakin gwamnan Ondo

Labari da duminsa: 'Yan majalisa 9 sun janye kansu daga yunkurin tsige mataimakin gwamnan Ondo

'Yan majalisar jihar Ondo tara sun tsame kansu daga kokarin tsige mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi.

Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, 'yan majalisar jihar Ondo sun fara shirin tsige mataimakin gwmanan jihar, Mr Agboola Ajayi.

A halin yanzu yan majalisar na tattaunawa a zauren majalisar a kan zargin saba dokokin aiki da ake yi wa mataimakin gwamnan.

Bayan tattaunawar, Majalisar ta cimma matsayar aike wa mataimakin gwamnan takardar sanar da tsige shi.

Jami'an 'yan sanda da na hukumar tsaro ta NSCDC sun mamaye harabar majalisar domin tabbatar da doka da oda.

KU KARANTA: Yadda Shehu Sani ya karba N4m a hannuna zai bai wa alkalai - Shaida

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel