Babu sauran mai dauke da kwayoyin cutar korona a Jigawa - Dr. Zakari

Babu sauran mai dauke da kwayoyin cutar korona a Jigawa - Dr. Zakari

Mun samu rahoton cewa, a halin yanzu babu sauran ko mutum guda mai dauke da kwayar cutar korona a jihar Jigawa da ke Arewa maos Yammacin Najeriya.

Mahukuntan lafiya a jihar sun sanar da cewa, babu sauran mai cutar a jihar kamar yadda kafar watsa labarai ta Freedom Radio ta ruwaito.

Dakta Abba Umar Zakari, kwamishinan lafiya kuma shugaban kwamitin kar ta kwana da gwamnatin jihar ta kafa kan yaki da cutar korona, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai.

A hirarsa da manema labarai a ranar Litinin, Dakta Zakari ya ce mutum daya kacal aka samu ya kamu da cutar a duk fadin jihar cikin tsawon kwanaki 14 da suka gabata.

Mutum dayan da aka samu ya koma jiharsa ta asali inda kwararrun lafiya ke ci gaba da kulawa da shi kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Badaru
Hoto daga fadar gwamnatin Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Badaru Hoto daga fadar gwamnatin Jigawa
Asali: Twitter

A yayin da ya ke tabbatar da nasarar da gwamnatin jihar ta samu a fagen yaki da cutar, Dakta Zakari ya ce a halin yanzu cibiyoyin killace masu cutar da aka tanada a fadin jihar sun zama fayau babu kowa a cikinsu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan fiye da watanni hudu da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar ta yadu a jihohi 36 da kuma babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, babu jihar da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, inda a baya bayan nan aka gano masu dauke da kwayoyin cutar karo na farko a jihar Cross River.

KARANTA KUMA: Cutar korona ta hallaka mutum 654 a Najeriya - NCDC

Kawo yanzu a duk fadin kasar, cutar ta harbi mutum 29,286, sai kuma mutum 11,828 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 654suka riga mu gidan gaskiya.

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 152,952 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluman Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 16,804 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

Taswirar fidda bayanai ta NCDC ta nuna cewa, tun bayan bullar cutar a jihar Jigawa, ta harbi mutum 318, yayin da ta hallaka mutum 10, sa'annan an sallami ragowar mutum 308 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel